in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin da kamfanonin kasashen waje suka zuba a kasar Sin cikin shekaru 5 da suka gabata ya wuce dalar Amurka biliyan 400
2010-11-09 19:59:17 cri
Bisa sabon rahoton da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayar a ran 8 ga wata, an yi hasashen cewa, tun daga shekarar 2006 zuwa yanzu, yawan jarin da kamfanonin kasashen waje suka zuba a kasar Sin kai tsaye zai kai dalar Amurka biliyan 420, wato za ta kai matsayi na biyu a cikin dukkan kasashen duniya, kuma tana kan matsayi na farko a cikin dukkan kasashe masu tasowa a cikin jerin shekaru 18 da suka gabata.

Wani jami'in ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya ce, yanzu, kamfanonin da baki 'yan kasuwa suka kafa a kasar Sin sun riga sun zama wani muhimmin tushe na raya kasar Sin, kuma na daya daga cikin hanyoyin samar da guraban aikin yi. Haka kuma, sun taka muhimmiyar rawa wajen kyautata ka'idojin yin takara a kasuwa da kuma fasahohin bunkasa sana'o'i daban daban, har ma suna sa kaimi ga kasar Sin da ta kara saurin yin gyare-gyare kan tsarinta na tattalin arziki. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China