in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hauhawar farashin abinci sakamakon takarar da ake yi a kasuwar kasar Sin
2010-11-09 19:19:00 cri
Ibrahim: Tun daga watan Oktoba, farashin kayayyaki irinsu shinkafa, garin alkama, ko man girki, dukkansu sun karu a kai a kai a kantunan zamani na biranen kasar Sin. A lokacin da mazauna birane suke damuwa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi, manoma kuma suna farin ciki ne sosai. A gundumar Wuchang ta lardin Helongjiang dake arewa maso gabashin kasar, wadda ta shahara sosai wajen noman shinkafa mai inganci, wani manomi Chang Zhan ya yi farin ciki, inda ya ce, "Yawan shinkafa da za mu iya samu a bana za ta yi kyau. Idan an kwatanta shi da na bara, matsakaicin yawan shinkafa da zan iya samu daga kowace hekta zai kai fiye da kilogram dubu 11."

Sanusi: Amma, Chang Zhan shi ma yana da damuwa. A lokacin da aka shiga watan Oktoba, kusan dai an yi ruwan sama a kullum. Ko da yake an riga an girbe shinkafa daga gonaki, amma har yanzu ba su kammala bushewa ba. Sakamakon haka, ba a iya cashe su ba. Hakan ya sa har yanzu babu wani dan kasuwa da ya tuntube shi kan maganar sayen shinkafa, kuma har yanzu Chang Zhan bai san farashin shinkafa na shekarar bana ba. Chang Zhan ya ce, zaben wani kyakkyawan lokacin sayar da shinkafa a gare shi ya kasance tamkar yin caca ce. Mr. Chang ya bayyana cewa, "Sabo da gwamnatinmu ta riga ta kulla kwangila tare da mu, za mu iya kwatanta farashin shinkafa da gwamnatin ta tsara cikin kwangila da na kasuwa. Farashin shinkafa ya kan yi kyau a lokacin sanyi, a wancan lokaci ne zan sayar da shinkafar dake cikin hannuna. Ina fatan farashin shinkafa zai yi kusan daidai da na bara. Idan farashin ya hau kadan, to, zan samu riba."

Ibrahim: Yanzu abin da ya sa manoma kamar Chang Zhan suka yi farin ciki shi ne, a hakika dai, farashin amfanin gona ya soma karuwa a kai a kai. Har ma farashin alkama da na masara da na shinkafa sun kai wani sabon mataki.

Sanusi: Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a watan Satumba na bana, farashin kayayyakin masarufi ya karu da kashi 3.6 cikin dari sakamakon hauhawar farashin abinci.

Ibrahim: Lokacin da manoma suka samu riba sakamakon hauhawar farashin amfanin gona, su kuma mazauna birane wadanda suke sayen abinci da sauran kayayyakin masarufi a kowace rana sun soma nuna damuwa. Amma kwararru wadanda ke nazari kan harkokin tattalin arzikin aikin gona sun nuna cewa, ya kamata farashin amfanin gona ya karu, sabo da shi ne hanya mafi kyau wajen karuwar yawan kudin shiga da manoma suke samu. Mr. Zheng Fengtian wanda yake nazari kan batutuwan da suka shafi raya aikin gona da yankunan karkara a jami'ar jama'a ta kasar Sin ya bayyana cewa, "A da, manoma ba su son noman hatsi sabo da farashin amfanin gona bai taka kara ya karya ba. Bayan hauhawar farashin abinci da kayan lambu a birane, a kan nuna damuwa da cewa, hakan zai kawo illa ga marasa karfi dake cikin al'umma, amma ba zai kawo illa ga masu hannu da shuni ba. A hakika dai, farashin amfanin gona a kasuwar kasar Sin ya yi kasa sosai. Ban da kudin da manoma suka kashewa lokacin da suke noman amfanin gona, idan yawan kudin da manomi ya iya samu daga Mu daya, wato abin da zai samu a kimanin hekta 0.067 zai iya kai kudin Sin yuan dubu 4 ko dubu 5, wannan sakamako ne mai kyau. Dole ne a tabbatar da cewa wadanda suke noman hatsi sun samu ribar da ta dace, hakan zai iya tabbatar da samar da isashen hatsin da muke bukata."

Sanusi: Ganin yadda farashin amfanin gona ke shafar manoma da mazauna birane, yaya za a iya samun daidaito tsakanin batun bunkasa yankunan karkara da na birane, wannan batu ne mai matukar muhimmanci.

Ibrahim: A cikin 'yan shekarun nan, lokacin da ake kara saurin raya birane, manoma da yawa sun yi kaura daga garuruwansu zuwa birane domin cin rani, amma yawan manoman da suke son ci gaba da yin aiki a kauyuka yana ragu a kai a kai. Amma, dole ne a tabbatar da samar da isashen abinci ga mutanen da yawansu ya kai fiye da biliyan 1.3 a kasar Sin. Sabo da haka, Sinawa da yawa suka gane cewa, dole ne a kara zuba kudade kan ayyukan yau da kullum da ake bukata a yankunan karkara, kuma dole ne a samar da tallafin kudi ga manoma domin sa kaimi ga manoma da su himmatu ga aikin gona a kauyuka. Bugu da kari, dole ne a kafa wani tsarin tabbatar da farashin abinci domin tabbatar da ingancin rayuwar mutane marasa galihu a birane.

Sanusi: Amma babban dalilin da ya sa hauhawar farashin abinci shi ne yawan hatsin da aka samu ya ragu a lokacin zafi, har ma lokacin da 'yan kasuwa suke sayen hatsi, sun daga farashin hatsin.

Ibrahim: Yawan hatsin da kasar Sin ta samu a lokacin zafi ya kai kimanin kashi 30 cikin dari bisa na jimillar hatsin da ta samu tsawon shekara daya. Bayan an shiga watan Oktoba, an soma girbin hatsin da aka noma a lokacin kaka. An yi hasashen cewa, farashin hatsin da ake saya a lokacin kaka shi ma zai karu kadan. Mr. Gao Shiquan, direktan sashen yankunan karkara na hukumar kula da harkokin abinci ta lardin Helongjiang, wato lardi mafi muhimmanci wajen samar da hatsi a kasar Sin ya bayyana cewa, "Yanzu 'yan kasuwa sun fi son sayen shinkafa da masara. Sakamakon haka, farashinsu zai karu bisa na bara." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China