A ran 7 ga wata, kakakin gwamnatin kasar Iraki ya bayyana wa manema labaru cewa, bisa wannan shirin kudurin da manyan jam'iyoyin siyasa na kasar suka samu a ran 6 ga wata, shugaban kasar Iraki Jalal Talabani zai ci gaba da rike mulkinsa na shugaban kasar, kuma firaministan kasar Nouri Kamel Al-Maliki zai ci gaba da zama firaministan na sabuwar gwamnatin kasar, jam'iyyar Iraqia List da ke karkarshin jagorancin tsohon firayim ministan kasar Ayad Allawi za ta zabi wani mutum da zai zama shugaban majalisar dokoki. Dubagh ya kara da cewa, jam'iyyun da suka samu wannan shirin kuduri sun hada da jam'iyyar TSLC da ke karkashin jagorancin Nouri Kamel Al-Maliki da jam'iyyun Na da Kurdistani da ke karkashin jagorancin 'yan shi'a, saidai jam'iyyar Iraqia List ba ta nuna amincewa ga wannan shirin kuduri ba. Ban da haka kuma, Dubagh ya shaida cewa, Nouri Kamel Al-Maliki da Ayad Allawi za su halaci taron da za a shirya a birnin Arbil a ran 8 ga wata, don yin shawarwari kan harkokin raba madafun iko.
Ya zuwa yanzu, jam'iyyun NA da KA da Iraqia List ba su nuna ra'ayoyinsu game da wannan shirin kuduri ba. Amma wani jami'in jam'iyyar Iraqia List ya bayyana wa manema labaru cewa, a ran 8 ga wata, Ayad Allawi zai jagorancin manyan jami'an jam'iyyar zuwa birnin Arbil don yin shawarwari kan shirin kudurin tare da bangarori daban daban.
Bisa halin da ake ciki, har yanzu jam'iyyar Iraqia List na ci gaba da rike mukamin firayim ministan kasar. A ran 7 ga wata, wata jaridar da ke karkashin jagorancin gwamnatin Iraki ta bayyana cewa, a gun taron da jam'iyyar Iraqia List ta shirya a ran 6 ga wata, shugabannin jam'iyyar sun nuna amincewa ga Nouri Kamel Al-Maliki na zai rike mukamin firayim ministan kasar, amma kuma jami'an jam'iyyar su kula da harkokin gwamnatin kasar. Amma wani kakakin jam'iyyar Iraqia List ya bayyana cewa, labarin da jaridar ta bayar bai dace da hakikanin halin ba.
Amma bisa halin da ake ciki, Nouri Kamel Al-Maliki ya fi Ayad Allawi dacewa da rike mukamin firayim ministan kasar Iraki. Akwai kujeru 325 a cikin sabon majalisar dokokin kasar, kuma Nouri Kamel Al-Maliki yana bukatar samu goyon baya daga kujeru 163 na dukkan kujeru na majalisar dokokin kasar don rike mukamin firaministan kasar. An iya cewa, a cikin taron da za a shirya a birnin Arbil a ran 8 ga wata, idan Nouri Kamel Al-Maliki ya samu goyon baya daga jam'iyyar NA ko jam'iyyar KA, zai iya ci nasarar samun akasarin kujeru. Saboda haka, Nouri Kamel Al-Maliki ya fi Ayad Allawi wajen rike mukamin firayim ministan kasar Iraki.