in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CRI ya shirya gasar kacici-kacici ta zabar biranen da suka shahara a harkokin yawon bude ido a kasar Sin
2010-11-03 08:51:47 cri
Ibrahim: A ran 19 ga wata da safe, an kaddamar da taron koli a game da batun raya biranen da suka shahara a harkokin yawon bude ido na kasar Sin a birnin Jinan, hedkwatar lardin Shandong dake gabashin kasar Sin. A gun wannan taron da ya kasance wani muhimmin aikin tabbatar da birane mafi jawo hankalin masu yawon bude ido a kasar Sin, an fi mai da hankali kan matsalolin da aka fuskanta lokacin da ake raya harkokin yawon bude ido a birane domin neman yadda za a tabbatar da hali na musamman ga kowane birni da yake kokarin raya sha'anin yawon bude ido, da kuma kokarin yada irin wadannan biranen kasar Sin a ketare.

Sanusi: A gun wannan taro, an tattauna kan irin gudummawar da ya kamata gwamnati ta bayar, da batun jawo hankalin masu yawon bude ido da huldar dake kasancewa tsakanin biranen dake raya sha'anin yawon bude ido da aikin jarida da kuma huldar dake tsakanin sha'anin bude ido da ci gaban tattalin arziki. A jawabin da ya gabatar, game da taimakon da ya kamata gwamnati ta bayar lokacin da ake raya sha'anin yawon bude ido, Mr. Yu Chong, shugaban hukumar kula da harkokin yawon bude ido ta lardin Shandong ya bayyana cewa, "Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta sanya sha'anin yawon bude ido a matsayin daya daga cikin muhimman ginshikan tattalin arzikin kasar, kana sana'ar zamani ce da jama'a za su iya jin dadinta. Sabo da haka, lokacin da ake raya sha'anin bude ido a birane, ya kamata gwamnati ta ba da jagorancin da ake bukata ga kokarin raya yawon bude ido ba tare da cikas ba. A ganinmu, gwamnati ta ba da jagoranci ne kawai, amma ba ta iya yin kome da kome da kanta ba, wato nauyin da aka dora mata shi ne raya kasuwa da kafa wani kyakkyawan muhallin raya wannan sha'ani bisa ka'idojin da aka gindaya lokacin da ake raya tattalin arziki irin na jari hujja."

Ibrahim: lokacin da ake bukatar shakatawa, abubuwa masu jawo hankalin mutane na wani birni yana da muhimmanci matuka. Don haka, yaya za a iya jawo hankalin masu yawon bude ido? Mr. Liu Deqian, mai nazarin harkokin yawon bude ido yana ganin cewa, "Ba ma kawai yanayin halittu da abubuwan tarihi da ayyukan yau da kullum na wani birni suna iya jawo hankalin masu yawon bude ido ba, har ma kokarin da wani birni ke yi yana iya jawo hankalin mutane, wato ya kamata birane wadanda suke son raya sha'anin yawon shakatawa su yi kokarin sanya masu yawon shakatawa su ji dadin yin ziyara a wajensu."

Sanusi: E, a hakika dai, bayan wani birni ya zama wurin da ya samu karbuwa daga wajen masu yawon shakatawa, tabbas ne zai iya jawo dimbin masu yawon bude ido. Sakamakon haka, a wasu lokuta, mazauna birnin da masu yawon bude ido za su ji dadin wannan birni tare. To, yanzu tambaya ita ce, yaya mazauna da masu yawon bude ido za su iya jin dadin zama tare a birni daya? Game da wannan batu, Shehun malami Dai Bin, wato shugaban cibiyar nazarin harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Ya kamata mu kasance masu saukin kai da mutunta jama'a. Wannan zai sa mu iya mayar da biranen da muke zama su zama tamkar biranen da masu sha'awar bude ido za su ji dadin shakatawa, musamman abin da ya shafi al'adunsu. Na kan fadi a kowane lokaci cewa, duk birnin da ya dace da zama ya kamata ya kasance birni mai dacewa da shakatawa."

Ibarahim: amma, lokacin da muke raya sha'anin yawon bude ido, yaya za mu iya magance hadarurruka iri iri dake faruwa, kamar matsalar kudi da ta auku a kasa da kasa domin kyautata ingancin sha'anin yawon shakatawa da jawo karin masu yawon bude ido na kasa da kasa a kasar Sin? Wannan ne batun da ake mai da hankali sosai a kai. Sabo da haka, a karkashin jagorancin ofishin yada labaru na gwamnatin kasar Sin da hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin, a watan Afrilu na shekarar bana, gidan rediyon kasar Sin, wato CRI ya shirya gasar kacici-kacici ta zabar birane guda 10 da suka shahara a harkokin yawon shakatawa a kasar Sin, inda masu karanta shafin intanet na CRI za su zabi wadannan birane 10. Mr. Ma Weigong, mataimakin babban editan CRI ya ce, "Gidan rediyon CRI yana watsa wa kasashen duniya bayanai daban daban game da kasar Sin, ciki har da bayanan da suka shafi yawon shakatawa na birane daban daban na kasar. Wannan wani muhimmin nauyi ne da aka dora wa gidan rediyon CRI da CIBN dake karkashinsa. Muna fatan masu sauraro da masu karanta shafinmu za su iya shiga wannan gasa domin yada bayanan birane masu yawon shakatawa na kasar Sin ga masu yawon shakatawa na sauran kasashen duniya."

Sanusi: e, haka ne, a karshen watan Nuwamba na bana, za a tabbatar da birane 10 daga cikin birane 20 wadanda suke takara a cikin wannan gasar kacici-kacici bisa kuri'un da masu karanta shafinmu suka jefa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China