in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin baje kolin duniya na Shanghai ya burge babban sakataren MDD sosai
2010-11-02 14:08:36 cri

A ran daya ga wata a birnin Shanghai, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, bikin baje kolin duniya na Shanghai wani gagarumin biki ne mai alama sosai, wanda ya bayyanawa duniya babban sakamakon da kasar Sin da jama'arta suka samu. Ya burge mutane kwarai da gaske.

Ban Ki-moon ya furta cewa, bikin baje kolin duniya na Shanghai ya wakilci hikimomin duniya baki daya, wanda ya tattara kasashen duniya daban daban a gu daya. Bayan haka, ya samar da fasahohi masu kyau wajen samun dauwamammen ci gaba.

Dadin dadawa, Ban Ki-moon ya ce, ko da yake an riga an kammala bikin baje kolin, amma za a yada ra'ayoyin bude kofa ga ketare, yin shawarwari, da musayar fasahohi a ko da yaushe.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China