Bisa labarin da BBC ya bayar, an ce, bikin EXPO na Shanghai ya zama wata hanyar shaida sakamakon da kasar Sin ta samu. A cikin labarin an kara da cewa, domin aiwatar da jigon bikin EXPO, gwamnatin birnin Shanghai ta yi amfani da motocin da ke yin amfani da wutar lantarki a lambun bikin EXPO, kuma ta gina na'urorin sanyaya daki mai tsimi makamashi da tsarin ingancin ruwan sha.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na AP na kasar Amurka ya bayar, an ce, kasar Sin ta kashe kudin Sin RMB yuan biliyan 28.6 wajen shirya bikin EXPO, kuma yawan kudin da ta samu dangane da bikin EXPO da yawon shakatawa ya wuce kudin Amurka dala biliyan 10.(Abubakar)