in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe bikin EXPO na Shanghai na shekarar 2010
2010-10-31 21:59:15 cri

A daren ranar 31 ga wata, an rufe bikin baje koli na Shanghai na shekarar 2010 da aka shafe kwanaki 184 ana yinsa, inda firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya sanar da nasarar rufe bikin.

Mataimakin firaministan kasar Sin, kuma daraktan kwamitin shirya bikin EXPO na shekararar 2010 ya yi jawabi a yayin bikin, inda ya bayyana cewa, bikin EXPO na Shanghai na hade da sakamakon da bil Adam ya samu ta fuskar wayewar kai, wanda ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin duniya da yawansu ya kai 246.

Mr. Jean-Pierre LAFON, shugaban hukuma mai kula da shirya bukukuwan baje koli a duniya ya bayyana a bikin cewa, bikin EXPO na Shanghai babbar nasara ce da aka samu, a sa'i daya kuma wani ci gaba ne da aka samu a fannin shirya bukukuwan EXPO.

Bayan haka kuma, wakilin kwamitin shirya bikin EXPO na Shanghai ya mika tuta ga wakili daga birnin Milan na kasar Italiya, birnin da zai karbi bakuncin bikin EXPO a shekarar 2015.

Bikin EXPO na Shanghai shi ne karon farko da aka shirya bikin EXPO a wata kasa mai tasowa. Tun bayan da aka bude bikin a ranar 1 ga watan Mayu, bikin ya jawo hankalin maziyarta daga kasar Sin da kasashen ketare fiye da miliyan 73, kasashe da kungiyoyin duniya da yawansu ya kai 246 sun hallara a bikin, inda suka kafa rumfunansu, tare da bayyana sakamakon da suka samu a fannin fasahohin zamani, da kuma manufofinsu ta fuskar neman dauwamammen ci gaba.

A wannan rana da yamma a birnin Shanghai kuma, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da shugabannin kasashe 7 da suka halarci dandalin tattaunawar manyan jami'ai da aka kira a bikin, ciki har da kasashen Lesotso, Nepal, Sri Lanka, Finland, da sauransu, wadanda suka taya murnar nasarar shirya bikin EXPO na Shanghai. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China