in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira dandalin tattaunawar manyan jami'ai a bikin EXPO na Shanghai
2010-10-31 17:18:58 cri

A ranar 31 ga wata, an kira dandalin tattaunawar manyan jami'ai a wajen bikin baje kolin duniya na EXPO da ke gudana a birnin Shanghai na kasar Sin, dandalin da ke da wani babban jigo na 'gyara birane da sabbin fasahohi tare da samun bunkasuwa mai dorewa', inda Mista Wen Jiabao, firaministan kasar Sin, ya halarci bikin bude dandalin tare da yin jawabi.

Mista Wen ya furta cewa, bikin EXPO na Shanghai da ke kokarin bayyana wani babban jigo na 'ingancin birni shi ne na rayuwa', wanda ya hada fasahohin da mutanen kasashe daban daban suke da su ta fuskar raya birane a waje daya, ta haka ya zama wani biki mai tasiri a tarihin bukukuwan baje kolin duniya, sa'an nan ya kasance wani gagarumin bikin da ya nuna samun nasarori, wanda ba za a iya mantawa da shi ba. Haka zalika, Mista Wen ya kara da cewa, bikin EXPO na Shanghai ya bayyana yadda bil Adama suke samun ci gaba da bunkasuwa, haka kuma ya nuna kalubalolin da suke fuskanta da damuwar da suke da ita. Don haka, da an ambaci yadda za a yi kokarin yada ra'ayin bikin EXPO, nufinsa shi ne yin kira ga mutanen duniya da su hada kai a kokarin tinkarar kalubaloli, tare da zummar tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a duniya.

Ban da haka kuma, Mista Wen ya yi nuni da cewa, yadda aka karbi bakuncin bikin EXPO cikin nasara, ya karfafa wa kasar Sin gwiwa wajen ci gaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje. Sa'an nan kasar Sin za ta tsaya kan hanyar raya kasa cikin lumana, tare da nuna sha'awar koyon fasahohi masu kyau daga kasashe daban daban, haka kuma za ta karfafa hadin kan da take yi da sauran kasashe a ci gaba da amfanawa junansu, don neman kara samar da gudumawa ga aikin ciyar da bil Adam gaba.

Sauran manyan jami'an da suka halarci bikin bude dandalin da aka shirya a ran nan sun hada da Ban Ki-moon, babban sakataren MDD, da Vicente Loscertales, babban sakataren hukuma mai kula da shirya bukukuwan baje koli a duniya. Mista Loscertales ya yi jawabi a wajen bikin da cewa, gwamnatin kasar Sin ta kula da aikin karbar bakuncin bikin EXPO yadda ya kamata, sa'an nan bikin EXPO da aka shirya a birnin Shanghai a wannan karo ya kasance wanda ya samu halartar bangarori daban daban na duniya, ta hakan ya aza wani ingantaccen harsashi wajen kara kyautata bukukuwan EXPO a nan gaba.

Ban da haka kuma, labarin da muka samu ya bayyana cewa, za a rufe bikin baje kolin duniya na Shanghai a daren ranar 31 ga wata. Insa za a shirya wani biki don rufe bikin baje kolin, bikin da shugabannin kasar Sin da wasu manyan kusoshi na kasashe daban daban za su halarta. An ce, a wajen bikin rufewar za a gwada wasannin fasaha, wadanda za su taimakawa masu kallo wajen maimaita yadda aka gudanar da bikin EXPO cikin yanayin annashuwa kwanaki 184 da suka wuce. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China