in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan kasashe 4 wadanda suka shahara kan sana'ar sarrafa manhaja sun taru a kasar Sin
2010-10-26 16:33:28 cri
Ibrahim: Sunayen kasashen Indiya da Ireland da Isra'ila dukkansu sun fara ne da harafi "I", kuma sun shahara sosai a sana'ar sarrafa manhaja. Sannan a cikin 'yan shekarun nan, ita ma kasar Sin ta samu ci gaba sosai a wannan sana'a ta sarrafa manhaja, har ma ta dauki wani muhimmin matsayi a sana'ar sarrafa manhaja a duniya. Yanzu yawan kayayyakin manhaja da kasashen Sin da India da Ireland da Isra'ila suke samarwa ya kai kashi 1 bisa kashi 5 na duk duniya, sakamakon haka, ake kiransu "kasashe 4 masu sarrafa manhaja". A bara, wakilan wadannan kasashe 4 sun gana da juna a birnin Nanjing na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, inda suka kulla "Sanarwar Nanjing" domin kokarin yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. A gun bikin baje kolin sana'ar sarrafa manhaja na kasa da kasa karo na 6 da aka yi a birnin Nanjing na kasar Sin, wakilan wadannan kasashe 4 sun sake saduwa, inda suka tattauna yadda za su yi hadin gwiwa domin cimma nasara tare.

Sanusi: A gun wannan biki, an shirya wani gagarumin biki na daban, wato an yi amfani da matsayin birnin Nanjing "shahararren birnin raya sana'ar sarrafa manhaja na kasar Sin". Mr. Alan Buckley, jami'in da ke kula da harkokin kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Ireland dake nan kasar Sin ya bayyana cewa, "Da farko, na taya birnin Nanjing murnar zama shahararren birnin dake kan gaba a fannin sana'ar sarrafa manhaja. Kasar Ireland tana kan gaba a duniya wajen nazarin sana'ar sarrafa manhaja. Muna fatan za mu iya yin hadin gwiwa da birnin Nanjing, har ma da dukkan kamfanonin nazarin kayayyakin mahanja na lardin Jiangsu."

Ibrahim: Jama'a masu sauraro, yawan mutanen kasar Isra'ila ya kai miliyan 7 da dubu dari 5, wato ya yi kusan daidai da na birnin Nanjing na kasar Sin, amma karfin nazarin kayayyakin sarrafa manhaja na kasar Isra'ila yana kan gaba a duk duniya. Duk da cewa tana kan gaba, amma a gun bikin baje koli na Nanjing, kasar Isra'ila ta nemi a yi hadin gwiwa tare da ita a fannin nazarin kayayyakin sarrafa manhaja. Mr. Jaun Cohen, shugaban kungiyar kasuwancin kasar Isra'ila dake kula da kasuwannin kasashen Asiya, kuma tsohon ministan kula da masana'antu da cinikayya na kasar Isra'ila ya ce, babu wata kasa da za ta iya zama a kan gaba a duniya a kullum a takarar da ake yi a kasuwa, inda Mr. Jaun Cohen ya nuna cewa, "Muddin kasashen Sin da Indiya da Isra'ila da Ireland suka kara yin hadin gwiwa, hakika za mu samu nasara. Kasar Isra'ila ta samu dimbin nasarori a bangaren kimiyya da fasaha, kuma tana da nagartattun masu kimiyya da fasaha da kyakkyawar kasuwa, amma duk da haka ba za su ishe mu ba. Halin da kasar Sin ke ciki ma ya yi kusan daidai da halin da kasar Isra'ila ke ciki. Kasar Sin tana da wata babbar kasuwa da isassun kudin da take zubawa kan aikin nazarin kimiyya da fasaha, amma ba ta da isashen karfin canza musu muhallin zama kayayyakin da za a iya sayar da su a kasuwa. Sabo da haka, ya kamata mu kara yin hadin gwiwa domin kokarin samun nasara lokacin da muke yin gagayya a kasuwa da kasashen Amurka da Turai da Japan."

Sanusi: Bayan shekara 1 da shirya taron wakilan wadannan kasashe 4, tuni suka samu sakamako. Mr. Amilam Saul, shugaban kungiyar kula da sana'ar sarrafa manhaja ta kasar Isra'ila ya gaya wa wakilanmu cewa, sun riga sun samu abokan yin hadin gwiwa a birnin Nanjing. Mr. Amilam Saul ya bayyana cewa, za a samar da ayyukan da za su dace da zamani guda 2 a birnin Nanjing.

"Daya daga cikinsu shi ne wani ayyukan sadarwa. Bayan da muka kammala wadannan ayyuka, saurin aikewa da bayanai ta waya zai kai 10G. sannan za mu samar da wasu ayyuka na daban. Bisa fasahar wannan ayyuka, za a iya yin amfani da wayar salula wajen biyan kudi maimakon katin banki da ake amfani da shi yanzu."

Ibrahim: Yanzu a kasar Indiya, akwai kamfanoni fiye da dubu 8 da suke nazarin kayayyakin sarrafa manhaja. Mr. Rajeh, Shugaban tawagar wakilan kamfanonin nazarin kayayyakin sarrafa manhaja ta kasar Indiya, kuma babban wakilin hadaddiyar kungiyar masana'antun kasar dake nan kasar Sin, ya ce, a kimanin shekara ta 2007, kasar Indiya ta soma neman kwangilolin samar da kayayyakin sarrafa manhaja ga kasashen waje cikin sauri, kuma ta samu nasara. Yanzu wasu kamfanonin sadarwa na zamani IT na kasar Indiya suna neman damar yin hadin gwiwa da takwarorinsu na lardin Jiangsu. A ganin Mr. Rajeh, wannan hanya ce mai wayo sabo da kamfanonin sadarwa na zamani IT na lardin Jiangsu suna samun ci gaba cikin sauri kamar yadda ake fata. Mr. Rajeh ya ce, "Sana'ar sarrafa manhaja tana samun ci gaba sosai a lardin Jiangsu. Kuma kamfanonin lardin Jiangsu suna da kyakkyawar damar yin hadin gwiwa da takwarorinsu na kasashen waje, ciki har da na kasar Indiya." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China