in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya liyafar cika shekaru 10 da kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika
2010-10-25 20:16:40 cri

A ranar 25 ga wata, a nan birnin Beijing, an shirya liyafar cika shekaru 10 da kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin da ministan harkokin wajen kasar Sin Yang Jiechi da jakadun kasashen Afrika da ke kasar Sin sun halarci wannan liyafa.

A yayin liyafar, Mr. Jia ya ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi, ya sa tsarin dandalin tattaunawar ya samu ingantuwa, kuma bangarorin biyu sun kara yin mu'mala a tsakaninsu. Game da kara raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, Jia Qinglin ya ba da shawarwari guda 4, Na farko kamata ya yi a yi la'akari da dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika bisa manyan tsare-tsare da lalubo sabuwar hanyar yin hadin gwiwa a tsakaninsu da kara cusa sabbin abubuwa cikin dangantaka dake tsakaninsu da inganta shawarwari don tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa.

A madadin jakadun kasashen Afrika da ke kasar Sin, shugaban tawagar jakadun kasashen Afrika a kasar Sin kuma jakadan kasar Togo da ke kasar Sin Nolana Ta-Ama ya ce, an samu kwalliya ta biya kudin sabulu a gun taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kuma ya jinjinawa matakan da kasar Sin ta dauka domin taimakawa kasashen Afrika, kuma yana fatan kasar Sin za ta tsaya kan manufar taimakawa kasashen Afrika a nan gaba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China