in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministar harkokin cikin gida ta kasar Afrika ta kudu ta yaba da gudummawar masana'antun kasar Sin a kasarta
2010-10-20 21:07:51 cri

A ranar 20 ga wata, karamin ofishin jakadancin Sin da ke kula da harkokin kasuwanci a kasar Afrika ta Kudu ya ruwaito kafofin yada labaru na kasar Afrika ta Kudu na cewa, kwanan baya, ministar harkokin cikin gida ta kasar Afrika ta kudu Nkosazana Dlamini Zuma ta kai ziyara birnin Shanghai, kuma a gun bikin rufe rumfar kasar Afrika ta Kudu a gun bikin Expo na Shanghai, gwamnatin Afrika ta Kudu ta yaba wa gudummawar da masana'antun kasar Sin suka bayar wajen raya tattalin arziki na kasar, kuma za ta ci gaba da nuna maraba ga masana'antun kasar Sin da su zuba jari a wannan kasa.

Madam Dlamini ta ce, kamfanin Huawei na kasar Sin ya riga ya kafa cibiyoyin nazari da sansanin samun bunkasuwa a kasar Afrika ta Kudu, kuma wannan ba ma kawai ya kara sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da kimiyya da fasaha a kasar Afrika ta Kudu ba, zai kara samar da guraben aikin yi da dama, gwamnatin kasar Afrika ta kudu za ta ci gaba da nuna maraba da kamfanin Huawei ta fuskar saka jari a Afrika ta kudu, kuma kasar za ta taimake shi domin raya kasuwanni a sauran kasashen Afrika.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China