in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mr. Chen Hailun da kayan kidan piano samfurin Hailun
2010-10-18 10:52:16 cri
Ibrahim: Lardin Zhejiang muhimmin lardi ne da ya yi suna a kasar Sin wajen raya tattalin arziki. A kwanan nan, wasu wakilan gidan rediyon CRI sun kai ziyara lardin, inda suka ziyarci wani kamfanin kera piano, wani nau'in kayan kida na Turai. Mr. Chen Hailun, shugaban hukumar direktocin wannan kamfani shi ne ya kafa shi. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wani bayani game da yadda yake tafiyar da wannan kamfanin kera kayan kida na piano.

Sanusi: malam Ibrahim, wannan kamfanin fa shi ne yake samar da kayayyakin kida na piano samfurin "Hailun" wanda yanzu ya yi suna sosai a kasar Sin. An kafa wannan kamfani ne a shekarar 1986 a birnin Ningbo na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Yanzu, yawan leburorin da suke aiki a wannan kamfani ya kai dari 8 ko fiye.

Ibrahim: amma, malam Sanusi, ka ga kayan kida na piano kayan kida ne na kasashen yammacin duniya. Muna ganin cewa, kasashen Turai ne suka shahara wajen samar da kayayyakin kida na piano masu inganci.

Sanusi: e, haka ne. Sabo da haka, ba abu ne mai sauki ba ga kamfanonin kera kayayyakin kidan piano na kasar Sin su sayar da kayayyakinsu a kasuwannin kasashen Turai. Amma, yaya kamfanin kera kayayyakin kida na piano samfurin Hailun na kasar Sin yake kokarin neman ci gaba a kasuwar cikin gida ta kasar Sin, kuma yaya ya yi suna a wasu kasuwannin kasashen duniya? Game da wannan batu ne, Mr. Chen Hailun, shugaban hukumar direktocin kamfanin Hailun ya bayyana cewa, "An soma kera kayan kida na piano ne a nahiyar Turai. Sabo da haka, piano kayan kida ne da ya samu asali daga kasashen yammacin duniya. Sun shafe kusan shekaru fiye da dari 3 suna kera kayan kida na piano. Amma an yi shekaru kusan dari 1 ne kawai ana kera su a nan kasar Sin. Sakamakon haka, a takaice dai, sun fi mu kwarewa wajen kera kayan kida na piano. Hakan ya sa muka gayyaci masana daga kasashen Turai domin su taimaka mana wajen kera kayan kida na piano. Masanan da muka gayyata sun zo ne daga kasashen Faransa da Amurka da Japan da Austria. Kuma sun kware sosai wajen yin zane-zane da fasahohin kera kayayyakin kida na piano."

Ibrahim: Tun daga shekarar 2001, kamfanin kera kayan kida na Hailun ya zuba makudan kudi domin shigo da injunan kera kayan kidan piano irin na zamani daga kasar Japan, sannan ya gayyaci Mr. Peter Veletzky, kwararre a fannin kera kayan kida na piano wanda ya zo daga Vienna da Mr. George Emerson wanda ya zo daga kasar Amurka, kuma ya kware sosai wajen zayyana salon kayan kida na piano da dai sauran masana daga wasu kasashen yammacin duniya. Dalilin da ya sa kamfanin Hailun ya shigo da wadannan masana shi ne ba ma kawai yana sayar da kayayyakinsa a kasuwar cikin gidan kasar Sin ba, har ma yana da shirin sayar da kayayyakinsa a kasuwannin kasashen yammacin duniya..

Sanusi: Yanzu, sannu a hankali kayayyakin kida na piano samfurin Hailun sa samun karbuwa a wajen al'ummar kasar Sin. Sabo da haka, yawan kayan kidan piano samfurin Hailun da ake sayarwa a kasar Sin yana ta karuwa. Game da shirin sayar da kayayyaki da kamfanin ya tsara, Mr. Chen Jianbin, mataimakin babban direktan kamfanin Hailun ya gaya wa wakilinmu cewa, "Bisa kididdigar da muka yi, yawan kayayyakinmu da ake sayarwa a kasuwannin kasashen waje ya karu daga kashi 14 zuwa kashi 60 cikin kashi dari bisa na bara, a waje daya, yawan kudin da muka samu sakamakon sayar da kayayyakinmu a kasuwar cikin gidan kasar Sin ya karu da kashi 60 cikin kashi dari."

Ibrahim: Ko da yake kamfanin kera kayan kidan piano na Hailun wani kamfani ne mai zaman kansa, kuma bai dade ba wajen kera kayan kida na piano, amma yana mai da hankali sosai kan ingancin kayayyakinsa. Sabo da haka, a watan Faburairu na shekarar 2006, fadar sarautar kasar Denmark ta zabi kayan kida na piano samfurin Hailun a matsayin kayan kidan piano da ake amfani da shi a fadar. Bugu da kari, a cikin gasannin da mujallar Diapason wadda ta kware sosai wajen shirya gasannin kayayyakin kida na piano a kasashen Turai ta shirya, kayan kida na piano samfurin Hailun ya shiga rukunin kayan kida mafi daraja. Wannan ne karo na farko da kayan kida na piano da aka kera a kasar Sin ya samu irin wannan lambar yabo. Game da wadannan gasanni, Mr. Chen Hailun ya yi alfahari da cewa, "A gun gasannin da aka shirya a tsakanin kasa da kasa a shekara ta 2008 da ta 2009, salon kayan gida biyu na kayayyakin kidan pianonmu sun samu lambobin yabo na zinariya. Ka sani, salo iri iri na kayan kida na kasashen Turai sun shiga wadannan gasanni biyu, amma, daga karshe dai, kayan kidan piano samfurin Schimmel na kasar Jamus da namu samfurin Hailun sun samu lambobin yabo na zinariya." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China