Rahoton da aka bayar ya shaida cewa, zuwa karshen shekarar bara, yawan kudin kayayyakin da ake cinikayyar a tsakanin Sin da Afirka ya zarce dala biliyan 91, hakan ya sa kasar Sin ta zama kawar kasashen Afirka wadda ta fi yin ciniki da su. Haka kuma yawan jarin da kasar Sin ta zuba a Afirka kai tsaye, da jarin da kasashen Afirka suka zuba kasar Sin, dukkansu sun kai kimanin dala biliyan 10. Ban da haka kuma, kasashe fiye da 50 ne suka amfana da tallafin da kasar Sin ta baiwa Afirka, hade da ayyuka fiye da 800, kuma wannan tallafi ya shafi bangaren gidaje, noma, aikin adana ruwa, sadarwa, zirga-zirga, jinya, da dai sauran fannoni daban daban.
Sa'an nan rahoton ya kara bayyana cewa, a nan gaba, Sin da Afirka za su yi kokarin habaka hadin kan da ke tsakaninsu zuwa wasu sabbin fannoni kamarsu hada-hadar kudi, masana'antu, yawon shakatawa, zirga-zirgar jiragen sama, da makamantansu. (Bello Wang)