in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Baki 'yan kasuwa sun kyautata zaton yanayin zuba jari na kasar Sin
2010-10-13 19:53:20 cri
Ibrahim: Lokacin da ake fuskantar kalubale iri iri kan makomar tattalin arzikin kasashen duniya, ko kamar yadda wasu mutane suka fadi cewa, wai yanayin zuba jari na kasar Sin ya lalace? Bayan da kasar Sin ta samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri cikin jerin shekaru 30 da suka gabata, ko wannan cigaban zai ragu? To, jama'a masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu duba batun yanayin zuba jari na kasar Sin.

Sanusi: A watan Satumba, an yi taron shekara-shekara na lokacin zafi na dandalin tattaunawar tattalin arziki na kasashen duniya wanda aka fi sani da taron Davos karo na hudu a birnin Tianjin, wani birnin dake bakin teku a arewacin kasar Sin. Yanzu, kamar yadda taron Davos na shekara-shekara na lokacin sanyi da a kan yi a kasar Switzerland yake, shi ma taron shekara-shekara na Davos na lokacin zafi da aka yi a kasar Sin har sau hudu ya zama daya daga cikin tarurrukan dandalin Davos da suka fi muhimmanci a duk duniya.

Ibrahim: Babban jigon taron shekara-shekara na Davos na lokacin zafi na shekarar 2010 shi ne "sa kaimi kan kokarin neman dawaumammen ci gaba". Ko shakka babu, kokarin sauya salon bunkasa tattalin arziki da kasar Sin ke yi ya kasance muhimmin batu da suka fi jawo hankalin mahalarta. Mr. Eckhartd Cordes, shugaban hukumar direktocin kamfanin Metro, kuma jami'in farko na kamfanin ya bayyana cewa, kamfanin Metro yana daya daga cikin kantunan zamani na uku mafi girma a duniya, kamfaninsa zai ci gaba da zuba jari a kasar Sin. Mr. Cordes ya ce, "Na sha kawo ziyara a kasar Sin ba adadi. Kasar Sin ta kan burge ni kamar yadda sauran mutane suke yi. Mun soma shiga kasar Sin a shekarar 1996, ya zuwa karshen bana, yawan kananan kantunan da muka kafa a kasar Sin zai kai 50, kuma za mu bude kantin intanet na farko a birnin Shanghai. A takaice dai, ni da mambobin hukumar direktocin kamfaninmu muna cike da imani sosai ga makomar kasar Sin."

Sanusi: Kasar Iceland wadda ta sha wahala sosai sakamakon matsalar hada-hadar kudi ta duniya ta samu sabuwar dama a kasar Sin, wato za ta iya samar da ayyukan yin amfani da makamashin ruwan zafi da ake samu daga karkashin kasa a kasar Sin. Sabo da haka, Mr. Olafur Ragnar Grimsson, firaministan kasar Iceland ya shirya wani taron manema labaru musamman lokacin da ake yin taron shekara-shekara na Davos a birnin Tianjin, inda ya bayyana wa 'yan jarida irin wadannan ayyukan da kasarsa da kasar Sin suke yi tare. Mr. Grimsson ya ce, "Kasarmu, wato kasar Iceland karamar kasa ce mai nisa sosai. Mu da kasar Sin muna hadin gwiwa kan muhimman batutuwa da dama, kamar batun samar da makamashi mai tsabta da aikin sa ido kan bala'in girgizar kasa da makamatansu wadanda suke da nasaba da duniya."

Ibrahim: Makamashi mai tsabta da Mr. Grimsson ya ambata shi ne daya daga cikn sabbin sana'o'in da kasar Sin take kokarin rayawa da kuma yin amfani da su a nan gaba bisa manyan tsare-tsare. Bisa manufofin da kasar Sin ta bayar a farkon shekarar da ake ciki, kasar za ta yi kokarin raya sana'o'in da ba za su gurbata yanayin duniya ba.

Sanusi: to, malam Ibrahim, yanzu bari mu tattauna wani batu na daban. A lokacin da kasar Sin, wato babbar kasa wajen samar da kayayyaki ga kasuwannin kasashen duniya take kokarin zama wata babbar kasa wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani domin sauya hanyar neman bunkasuwa, wasu kasashen duniya sun taba nuna damuwa cewa, ko kasar Sin za ta canja manufofin yin amfani da jarin kasashen waje? Game da wannan tambaya, lokacin da yake hira da masu tafiyar da kamfanoni wadanda suka halarci taron shekara-shekara na Davos na lokacin zafi a birnin Tianjin, Mr. Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin 'yan kwanakin nan, wasu mutane suna tattaunawa kan batutuwan kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani da kasar Sin ke yi, da batun kiyaye ikon mallakar fasaha a kasar. Ba kuskuren da kamfanonin kasashen waje suke yi ba, ana irin wannan tambaya ne sabo da ba su bayyana musu manufofinmu kamar yadda ya kamata ba. Sabili da haka, Mr. Wen ya jaddada cewa, kasar Sin na kokarin samar da wani kyakkyawan muhallin zuba jari ga baki 'yan kasuwa a kowane lokaci, kuma tana kokarin kiyaye ikon mallakar fasaha, inda Mr. Wen ya ce, "bisa dokokin kasar Sin, dukkan kamfanonin da aka yi wa rajista, kuma aka kafa su a kasar Sin, sun kasance tamkar kamfanonin kasar Sin ke nan. Kuma Kayayyakin da suke samarwa kayayyaki ne kirar kasar Sin, sannan sabbin kayayyakin da suka kirkiro kayayyaki ne da kasar Sin ta kirkiro. Dukkan kamfanoni masu jarin kasashen waje da aka yi wa rajista a kasar Sin za su iya more manufofin da kamfanonin kasar Sin suke morewa, kuma za su yi zama daidai wa daida."

Ibrahim: Wannan maganar da Mr. Wen ya yi ta bai wa baki masu zuba jari imani da tabbacin baje hajojinsu a kasuwar kasar Sin ba tare da wata fargaba ba. Mr. Davis Jin, shugaban hukumar direktocin kamfanin ba da shawara na Boston ya ce, babu alamar da ta nuna cewa, manyan kamfanoni suna rage yawan jarin da suke zubawa a kasar Sin.

"Firaminista Wen ya yi nazari kan yadda ake raya tattalin arzikin kasar Sin a cikin 'yan shekarun nan, kuma yaya za a yi amfani da sabuwar damar da aka samu da kuma yadda za a magance kalubalen da za su bullo a nan gaba cikin nasara? Bakin kamfaninmu suna cike da imani ga kasuwar kasar Sin. Ban ga ana rage yawan jarin da ake zubawa a kasar Sin ba, sai dai ma ana ci gaba da zuba jari a kasar. A cikin dogon lokaci mai zuwa, kasar Sin za ta kasance wata muhimmiyar kasuwa ga kamfanoni masu jari daga kasashen waje."

Sanusi: A hakika dai, kididdigar da aka bayar ta shaida ra'ayin Mr. Jin Weidong. Ya zuwa yanzu, kamfanoni 470 daga cikin kamfanoni 500 wadanda suka fi karfi a duniya sun riga sun kafa rassansu a kasar Sin. Bugu da kari, ya zuwa karshen watan Yuli na bana, jimillar yawan jarin kasashen waje da aka zuba a kasar Sin ta kai dalar Amurka biliyan 1050, sakamakon haka, kasar Sin tana matsayin farko cikin jerin shekaru 18 na farko wajen shigar da jarin kasashen waje.

Ibrahim: Mr. David Michael wanda ya kafa kamfanin ba da shawara na Boston, kuma babban direktan kamfanin yana ganin cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, sabuwar karuwar tattalin arzikin kasashen duniya ita ce farfadowar birane na yankuna wadanda suke samun ci gaba cikin sauri a halin yanzu. Sabo da haka, kasar Sin ta kasance wani muhimmin dandali da bai kamata a yi watsi da shi ba. Ayyukan raya birane da kokarin bunkasa kasuwannin cikin gida za su samar da wata sabuwar damar gudanar da harkokin yin kasuwanci. Mr. David Machael ya ce, "A takaice dai, ina cike da imani ga ci gaban tattalin arziki ba tare da wata tangarda ba. Tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasuwa sakamakon kokarin neman ci gaba cikin daidaito tsakanin yankuna daban daban da manufofin raya bukatun da ake da su a kasuwannin cikin gida da kasar ke aiwatarwa. Yanzu jawan kudaden da ake kashewa a kasuwar cikin gida ta kasar Sin ya kai kashi 36 cikin dari kawai bisa na jimillar GDP, amma irin wannan adadi ya kan kai kimanin kashi 60 cikin kashi dari a sauran kasashen duniya masu arziki. Sabo da haka, kokarin raya kasuwannin cikin gida da kasar Sin ke yi zai taka muhimmiyar rawa wajen neman bunkasa tattalin arziki cikin daidaito a tsakanin yankuna daban daban na kasar Sin. Kuma ko shakka babu, za ta fuskanci matsaloli da kalubale iri iri, amma muna da imani ga kasar Sin wajen daidaita su." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China