in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Sin da Afirka su kara yin hadin gwiwa
2010-10-12 20:10:02 cri

Ran 12 ga wata, Mr. Chen Deming ministan kasuwanci na kasar Sin ya rubuta wani sharhi a jaridar "People's daily" domin murnar cika shekaru 10 da kafa dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka, ya bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen Sin da Afirka bisa ka'idar "moriyar juna", domin amfamnin jama'arsu.

Mr. Chen Deming ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, an yi kokari domin aiwatar da matakai daban daban da aka tsara kan fannonin tattalin arziki da ciniki wadanda suka ba da gudummawa a zahiri ga bunkasuwar kasashen Sin da Afirka, kuma ya sami kurbuwa sosai daga kasashen Afirka. Idan ana son sa kaimi ga sabuwar huldar abokantaka da ke tsakaninsu, da kuma ci gaba da moriyar juna, da farko, ya kamata a karfafa kyakkyawan sakamakon da aka samu, wato kokarin shimfida matakan da aka tsara. Na biyu shi ne kyautata tsarin yin hadin gwiwa, tare da kafa tsarin yin hadin gwiwa kan fannoni daban daban. Na uku, fadada fannonin yin hadin gwiwa, kamar fannonin hada-hadar kudi, da kasuwanci, da sufurin kayayyaki, da zirga-zirga, da makamashi marasa gurbata muhalli. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China