in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka na kara bunkasa huldodin bangarorin biyu
2010-10-11 17:23:46 cri

Ranar 10 ga watan Oktoban shekara ta 2000, bisa ka'idojin da suka shafi nuna sahihanci, abokantaka, gami da goyon-baya ga juna, da neman bunkasuwa tare, kasar Sin da kasashen Afirka sun yanke shawarar kafa dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka, haka kuma sun shirya taron ministoci a karo na farko a nan birnin Beijing, lamarin da ya shaida cewar, dadaddiyar dangantakar zumunci ta hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka ta shiga wani sabon mataki a tarihi. Ranar 11 ga watan da muke ciki, Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta fitar da wani bayani da ministan harkokin wajen kasar Yang Jiechi ya rubuta, inda ya waiwayi irin dimbin nasarorin da wannan dandalin tattaunawa ya samu cikin shekaru 10 da suka gabata, kuma ya bayyana shawarwari game da yadda za'a ci gaba da raya dandalin a nan gaba.

Bayanin Mista Yang ya ce, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin da kasashen Afirka sun kafa wani cikakken tsarin hadin-gwiwa a tsakaninsu, wanda ya shafi siyasa, tattalin arziki, zaman rayuwar jama'a, al'adu da sauran fannoni, har ma wannan dandali ya samu muhimman nasarori a fannoni da dama:

Na farko, inganta dadadden zumunci, da raya dangantakar Sin da Afirka. Bugu da kari, dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka yana mayar da hankali kan dadaddiyar dangantakar abokantaka tsakanin bangarorin biyu, da rattaba hannu kan takardun da suka shafi daidaiton da suka cimma a kan huldodinsu gami da muhimman batutunwa kasa da kasa. Dandalin tattaunawar ba ma kawai ya karfafa nasarorin da Sin da Afirka suka samu ba a fannin yin mu'amala cikin fiye da rabin karnin da ya gabata, har ma ya samar da ingantaccen tushen siyasa ga hadin-gwiwarsu.

Na biyu, dandalin tattaunawar ya sa kaimi ga mu'amalar Sin da Afirka a fannin siyasa, da kara samun fahimtar juna. A yayin tarurrukan ministoci da dama na dandalin, an samu halartar shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka daban-daban, abun da ya bayar da babbar gudummawa ga mu'amala tsakanin manyan jami'ai na Sin da Afirka.

Na uku kuwa shi ne, sa kaimi ga hadin-gwiwar Sin da Afirka a dukkan fannoni. Sakamakon dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da Afirka, hadin-gwiwar bangarorin biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya na kara zurfafa kwarai da gaske, haka kuma kasar Sin na kara zuba jari a kasashen Afirka. Har wa yau kuma, cudanyar da ake yi tsakanin mata, matasa, kungiyoyin da ba na gwamnati ba, gami da masana na kara samun ingantuwa.

Na hudu shi ne, kasar Sin ta kara tallafawa kasashen Afirka, da mayar da hankali kan raya ci gabansu. Kasar Sin tana maida hankali a kan inganta karfin kasashen Afirka wajen neman ci gaba mai dorewa, a kokarin raya tattalin arzikinsu, da bayar da gudummawa a fannonin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen Afirka.

Na biyar wato na karshe shi ne, Sin da Afirka suna kara hada kai da taimakawa juna. Kasar Sin da kasashen Afirka su kan bayyana ra'ayoyinsu a kan halin da ake ciki a duniya, da kokarin kiyaye moriyar kasashen dake tasowa, lamarin dake da babbar ma'ana ga kafa wani sabon tsarin siyasa da tattalin arziki a duniya baki daya.

A cikin wannan bayanin da ministan harkokin wajen kasar Sin Yang Jiechi ya rubuta kuma, ya ce, shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 10 cif da kafa dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka. Sakamakon wannan dandalin tattaunawa, labuddah huldodin Sin da Afirka za su ci gaba da samun bunkasuwa a nan gaba!(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China