in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar rumfar Uganda a bikin EXPO na Shanghai
2010-10-09 19:31:16 cri

Ranar 9 ga wata rana ce ta rumfar jamhuriyar Uganda a bikin baje kolin kasa da kasa da ake yi yanzu a birnin Shanghai na kasar Sin. A wannan rana, Mr. Serapio Rukundo ministan harkokin yawon shakatawa na kasar Uganda da Mr. Zhu Shanzhong mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin sun halarci bikin taya murna tare da yin jawabi.

Mr. Serapio Rukundo ya nuna cewa, a cikin shekaru 48 tun bayan aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Uganda da Sin, huldar da ke tsakaninsu ta sami ci gaba sosai. Yana fatan biki EXPO zai sa kaimi ga hadin gwiwar da ke tsakaninsu kan fannonin siyasa, tattalin arziki, zaman al'umma, al'adu da kimiyya da fasaha. Mr. Rukundo yana ganin cewa, bikin EXPO na Shanghai ya sami nasara sosai, ya ba wa kasashe daban daban da su nuna al'adun kansu, ya sake ba da kwarin gwiwa ga mutanen da ke fama da matsalar tattalin arziki.

Mr. Zhu Shanzhong ya ce, babban taken rumfar kasar Uganda shi ne "manufar bunkasuwar birane a kasar Uganda", wannan ya nuna ni'imtattun wurare daban daban a yankin karkara da birane a kasar Uganda.

Ban da haka kuma, a gun bikin murnar ranar, 'yan wasa da suka zo daga kasar Uganda sun yi raye-raye masu kayatarwa sosai, kide-kide mai sa kuzari da raye-raye masu karfi sun sami maraba sosai daga masu kallo. [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China