in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da raya hadin gwiwa da kasashen Afrika
2010-10-09 17:19:59 cri

A ranar 9 ga wata, a gun taron manema labaru da ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin ta shirya a birnin Beijing game da cika shekaru 10 da kafa taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wani jami'in kasar Sin ya bayyana cewa, nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da fadada hadin gwiwa da kasashen Afrika, don cimma burin samun bunkasuwa tare.

A gun taron, direktar kula da yankunan yammacin kasashen Asiya da Afrika ta ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Madam Zhong Manying ta ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, gwamnatin Sin ta dauki matakai da dama don aiwatar da yarjejeniyar da aka daddale a gun taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika cikin tsanaki, ciki har da yafe wa kasashen Afrika basusuka da kara ba su gudummawa da horar da kwararru gare su. Haka kuma kasar Sin ta yi hobas domin taimakawa kasashen Afrika wajen rage talauci da aikin jinya da kiwon lafiya da ilmi da horaswa da sauran manyan ayyukan da ke shafar zaman rayuwar al'umma, kuma ta tashi tsaye domin nuna goyon baya ga kamfanonin kasar don su shiga cikin aikin raya manyan ayyuka tamkar wutar lantarki da hanyoyin kasa da hanyoyin jiragen kasa da aikin gona a kasashen Afrika.

Haka kuma, mataimakiyar direktar da ke kula da harkokin taimakawa kasashen waje a ma'aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin Madam Gao Yuanyuan ta ce, tun daga shekarar 2000 zuwa shekarar 2009, jimillar kudin rance da agajin jin kai da kasar Sin ta samar wa kasashen Afrika ta karu har sau 5. Madam Gao ta ce, gwamnatin Sin za ta sa himma domin aiwatar da sabbin matakan taimakawa kasashen Afrika, don ba da tabbaci ga cimma burin kammala aikin taimakawa kasashen Afrika tun da wuri.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China