in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar rumfar Cape Verde a bikin EXPO na Shanghai
2010-10-08 20:59:03 cri

Ranar 8 ga wata rana ce ta rumfar jamhuriyar Cape Verde a bikin baje kolin kasa da kasa da ake yi yanzu a birnin Shanghai na kasar Sin. A wannan rana da yamma, an yi wani kasaitaccen biki don murnar ranar, inda shugaban jamhuriyar Cape Verde da shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta birnin Shanghai suka yi jawabi.

Pedro Pires, shugaban jamhuriyar Cape Verde ya ce, halartar bikin baje kolin kasa da kasa da ake yi a birnin Shanghai wata kyakkyawar dama ce ga Cape Verde ta nuna ci gabanta da kuma yi musayar al'adu da sauran kasashe. Yanzu haka Cape Verde na kokarin raya birane na zamani, ta yadda za su dace da rayuwar al'umma, kokarin da ya zo daya da manufar bikin na Shanghai, wato "birni mai kayatarwa da zaman rayuwa mai inganci". A ganinsa, bikin da ake yi zai iya karfafa mu'amala tsakanin kasar Cape Verde da ta Sin.

Feng Guoqin, shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta birnin Shanghai ya ce, bikin baje kolin kasa da kasa da ake yi a Shanghai ya kasance wata gadar fahimtar juna tsakanin jama'ar Sin da ta Cape Verde, kuma tabbas ne zai karfafa dankon zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

A gun bikin murnar ranar, 'yan wasa da suka zo daga Cape Verde sun yi raye-raye masu kayatarwa sosai, wadanda suka fadakar da masu kallo a kan wannan kasa mai ni'ima da ake kira Cape Verde. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China