A cikin jawabin da Ehouzou ya yi, ya jinjina wa goyon baya da kasar Sin ta bayar domin taimakawa kasar Benin wajen halartar wannan taro. Ya ce, goyon baya da gwamnatin Sin ta bayar, ya bayyana dangantakar sada zumunci da ke tsakanin kasashen biyu. Yana ganin cewa, bikin Expo na Shanghai ya ba da wata kyakkyawar dama ga kasar Bini, don nuna albarkatun yawon shakatawa da ni'imtattun wurare a rumfar kasar.
A cikin nasa jawabi, Hua Junduo ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen Sin da Benin ya bunkasa cikin hanzari, kuma ya samar da hakikanin moriya ga jama'ar kasashen biyu. Ya yi imani cewa, bikin Expo na Shanghai ba ma kawai zai kara fahimtar da kasashen duniya game da Benin ba, har ma zai zama tamkar wata gada ce, ta ingiza mu'amala da hadin gwiwa da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu.
Haka kuma, wasannin kide-kide da raye-raye da masu wasan fasaha na jamhuriyar Benin suka nuna, sun samu karbuwa a tsakanin jama'a.(Bako)