Bisa labarun da manema labaru suka samu daga taron tattaunawar dokokin shari'a a karo na 2 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, an ce, kasar Sin da kasashen Afrika sun sauke nauyin dake kansu domin gudanar da shari'a a tsakaninsu, har da kai sammaci da gudanar da bincike da samun shaidu da bin bahasi wajen shari'a. Haka kuma, in akwai hali, za a dinga mayar da masu aikata laifi zuwa gida don ci gaba da daukar matakan kara ko yin hukunci a kansu.(Bako)