in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin ranar rumfar kasar Sin a yau a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-10-01 16:45:34 cri

A yau juma'a 1 ga wata da safe ne, aka yi bikin ranar rumfar kasar Sin a yau a babban dakin cibiyar farfajiyar bikin EXPO dake Shanghai, manyan jami'ai fiye da 700 na cikin gida da na waje sun halarci bikin. Zaunanen wakilin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo, da sakataren hukumar nune-nune ta kasa da kasa Loscertales sun yi jawabi a gun bikin.

Wu Bangguo ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, bikin EXPO na Shanghai gagarumin bikin kasa da kasa ne da aka yi a kasa mai tasowa a karo na farko. Kana Mr. Wu ya jaddada cewa, a cikin shekaru fiye da 30 da kasar Sin ke gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, tattalin arzikin kasar ya samu bunkasuwa cikin sauri, an samu kyakkyawan sakamako a fannoni da yawa, ya zuwa shekarar 2020, kasar Sin za ta cimma burin kafa al'umma mai wadata wadda jama'ar Sin fiye da biliyan daya za su ji dadin zama a ciki. Ya kara da cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, ko da yake kasar Sin ta gamu da wahalhalu da yawa a yayin da take neman samun bunkasuwa, amma tana da cikakken imani kan samu kyakkyawar makoma.

Bugu da kari, Mr. Wu Bangguo ya ce, kiyaye zaman lafiya a duniya nauyi ne dake kan kasar Sin, kuma ya aza harsashi ga bunkasuwar kasar Sin. Jama'ar kasar Sin sun taba fama da talauci, suna fatan za su samu wadata domin jin dadin zaman rayuwarsu, kana sun kuduri niyyar neman samun bunkasuwa, kuma ba wanda ke iya canja ra'ayinsu kan wannan kyakkyawar manufa.

Loscertales ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, duk da cewar ba a kawo karshen bikin EXPO na Shanghai ba tukuna, amma bikin ya kafa sabon tarihi a fannoni da yawa. Kasar Sin tana nuna kwarewa sosai wajen zama mai masaukin wannan gagarumin bikin kasa da kasa, kuma ta cika alkawarinta yadda ya kamata. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China