in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a Urumqi
2010-09-30 17:37:40 cri
Ibrahim: Taron tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya da bikin baje koli taro ne na shekara-shekara da a kan yi a jihar Xinjiang. Kuma wannan shi ne karo na 19 da aka shirya wannan bikin da aka kaddamar a ran 1 ga watan Satumba, inda aka kwashe kwanaki 5 ana yinsa a Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang a bana. A gun bikin da aka yi a bana, jimillar kudaden kwangilolin da aka kulla ta kai fiye da kudin Sin yuan biliyan dari 1. Bugu da kari, wannan ne karo na karshe da aka shirya wannan taron tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya a Urumqi, tun daga shekara mai zuwa, za a canza sunan bikin ya zuwa bikin baje koli na Asiya da Turai, wato zai fuskanci sabbin kasuwannin kasashen duniya gaba daya.

Sanusi: A cikin shekaru 19 da suka gabata, mutanen jihar Xinjiang su kan nuna kaunarsu ga wannan taron tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya na Urumqi. Dattijo Wufur Riheman, wanda ya kware wajen kera kayayyakin hannu wanda ya fito daga gundumar Yingjisha dake kudancin jihar Xinjiang. Ya riga ya halarci wannan taron tattaunawa har sau 18. Dittijo Wufur ya ce, kamfaninsa ya samu ci gaba ne sakamakon ci gaban wannan taron tattaunawa. "Lokacin da na halarci wannan biki a karo na farko, ba ma kawai ire-iren kayayyakin da muka samar sun yi kadan ba, har ma ba su da inganci sosai. Bayan da na ci gaba da halartar wannan biki, yanzu kowa ya san kayayyakinmu, kuma muna sayar da kayayyakinmu da kuma samun riba kamar yadda muke fata."

Ibrahim: madam Shan Xiumei wadda take yin mutum-mutumin atamfa ta gaya wa wakilinmu cewa, an soma sani da kuma nuna sha'awar mutum-mutumin atamfa da ta yi ne a gun bikin baje koli na Urumqi. Madam Shan ta ce, "A da, ba a san irin kayayyakin da na yi ba. A gun wannan bikin baje koli na Urumqi ne, aka soma sanin mutum-mutumin da na yi. Musamman a gun bikin baje koli da aka yi a shekarar 2004, ba zato ba tsammani, an gabatar da kayayyakinmu ga baki 'yan kasuwa cikin sauri."

Sanusi: Ba ma kawai a kan yi nune-nunen kayayyakin da jihar Xinjiang kawai ke samarwa a gun bikin baje koli na Urumqi ba, har ma an samar da kyakkyawar damar yin kasuwanci ga 'yan kasuwa. A gun bikin baje koli na Urumqi na karo na 19 da aka yi a farkon watan Satumba na bana, wakilinmu ya sadu da wani dan kasuwa, mai suna Mr. Yan Junjie wanda ya zo daga yankin Hongkong na kasar Sin. Mr. Yan ya ce, ya riga ya halarci wannan biki har sau uku. Kuma a gun wannan biki ne ya samu damar zuba jari a jihar Xinjiang. Mr. Yan Junjie ya bayyana cewa, "Na sani cewa, wannan ne karo na karshe da aka shirya bikin baje koli na Urumqi. Kamfaninmu ya riga ya zuba jari a jihar Xinjiang, kuma na taba halartar wannan bikin baje koli a baya. Muna fatan kamfaninmu zai iya zuba karin jari a jihar Xinjiang, har ma a yankunan Asiya na tsakiya."

Ibrahim: A gun wannan bikin baje koli na Urumqi na karshe, 'yan kasuwa da kamfanoni da suka fito daga kasashe 22 da yankunan Taiwan da Hongkong na kasar Sin sun yi hayar rumfuna da dama da za su baje hajojinsu. A karon farko yawan rumfunan da baki 'yan kasuwa da yawansu ya kai fiye da dubu 1 suka yi haya ya wuce dari 1.

Sanusi: Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur ta kasar Sin tana makwabtaka da wasu kasashen Asiya na tsakiya. Sabo da haka, suna son kara fahimtar juna da yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Sabo da haka, wasu yankunan jihar Xinjiang sun yi kokarin neman damar yin hadin gwiwa da kasashen da suke makwabtaka da juna. Birnin Tacheng na jihar Xinjiang yana makwabtaka da kasar Khazakstan. Mr. Zou Yiwei, mataimakin magajin birnin Tacheng ya fadi cewa, "Muna kokarin tuntubar bangaren kasar Khazakstan. Tun ran 2 ga watan Disamba na shekarar 2009, aka bude wata kasuwa a birnin Tacheng ga mazauna Khazakstan. Kuma suna iya ziyartar wannan kasuwa na kwana daya ba tare da takardar izinin shiga kasa ba, wato visa. Yanzu muna kokarin neman izinin ba su kwanaki uku na kawo wa duk birninmu ziyara ba tare da visa ba."

Ibrahim: Tun daga shekarar 2011, wannan bikin baje koli na Urumqi da aka yi shekaru 20 ana yinsa a jihar Xinjiang zai zama wani babban bikin baje koli na kasar Sin da kasashen Asiya da Turai. Kuma za a kara bude kofarsa ga yankunan da ke yamma da kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China