in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan ranar cika shekaru 61 da kafa Jamhuriyyar Jama'ar kasar Sin
2010-09-30 16:29:43 cri
Jama'a masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Yau rana ce ta cika shekaru 61 da kafa Jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. Dukkan jama'ar kasar suna murnar wannan rana. Amma sauran kasashen duniya fa? Yaya su kan yi a wannan rana? Yanzu bari mu saurara.

Bikin murnar ranar kafa kasa na da muhimmanci sosai ga kowace kasa, amma kowace kasa tana da sunan da take kiran wannan rana. Wasu kasashe su kan kira wannan rana da sunan "Ranar kafa kasa", wasu kuma sun kira shi "Ranar samun 'yancin kai", ko kuma "Ranar jamhuriyyar kasa" da dai makamantansu.

A daidai wannan rana, a kan gudanar da bukukuwa iri-iri domin murnar wannan rana. Gwamnatin kasa ta kan gudanar da shagulgula. Shugabannin kasa, ko ministan harkokin waje su kan jagoranci wannan biki, tare da gayyatar jakadun kasashen dake wurin da sauran muhimman baki. Duk da muhimmancin wannan rana wasu kasashe ba sa shirya irin wadannan shagulgula, kamar Amurka, Birtaniya, da sauransu.

Kamar yadda kasar Sin take yi, ranar daya ga watan Oktoba rana ce ta samun 'yancin kan kasar Nijeriya, wadda kuma ta kasance wata tsohuwar kasa a nahiyar Afirka da ta fi yawan jama'a. Kasar Nijeriya tana da dogon tarihi na sama da shekaru 1000 da al'adu masu kayatarwa. A cikin shekaru 100 da suka gabata, Birtaniya ta yi mulkin mallaka a can. Amma bisa kokarin jama'ar kasar ba tare da kasala ba, a karshe aka samu 'yancin kan kasar Nijeriya a ran daya ga watan Oktoba na shekarar 1960.

A kasar Amurka kuma, an tsayar da ranar 4 ga watan Yuli na kowace shekara a matsayin ranar kafa kasa. A daidai wannan rana, mutane su kan gudanar da bukukuwan murna da shirya zanga-zanga. Kullum wadanda su kan shirya irin wannan zanga-zanga a wannan rana, su kan yi ado iri daban daban. Wasu su kan yi kide-kide, da raye-raye, da wake-wake a tituna. Bayan kammala zanga-zangar, mutane su kan hallara a lambun shan iska ko wasu wurare domin murnar wannan rana tare da juna.

A kasar Vietnam, a kan yi murnar bikin irin wannan rana ne a ran 2 ga watan Satumba. A daidai wannan rana, a kan gudanar da gagaruman bukukuwa a birnin Hanoi, hedkwatar kasar, tare da duba jerin faretin sojojin kasar da yin zanga-zanga. Kafin wannan rana, gwamnatin kasar Vietman ta kan ba da sanarwa ga jama'a dake birane da larduna na kasar, a kokarin ba da umurnin murnar wannan rana. A kullum, a kan gudanar da gagarumin biki, da duba jerin faretin sojoji, da yin zanga-zanga. Gidajen telibiji da na rediyon kasar su kan gabatar da wadannan bukukuwa kai tsaye. A ran 2 ga watan Satumba da dare, a kan yi wasan wuta a birane daban daban na kasar Vietnam.

Sai dai a kasar Norway, a kan yi bikin murnar wannan rana a ran 17 ga watan Mayu na kowace shekara. A wannan muhimmiyar rana, mutane sama da dubu daya su kan sa kayan gargajiya suna murna a tituna. Daga yarinya zuwa tsohuwa, su kan sa siket masu launuka iri-iri, kamar ja, fari, baki, kore da dai sauransu. Kuma kowa ya kan sa abin ado mai kyan gani a gaban jiki. Maza kuma su kan sa riguna iri daban daban.

To, jama'a masu sauraro, a wannan muhimmiyar rana, dukkanmu Sinawa muna fatan kasar Sin za ta samu ci gaba mai kyau, tare da bunkasa dangantakar abokantaka tsakaninta da kasashenku yadda ya kamata. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Jama'a masu sauraro, a makon jiya, mun samu sakwanni da dama daga wajenku, kamar mai sauraronmu a kullum malama Fatima Musa Abbas a Nijeriya, inda ta bayyana mana cewa, "Da fatan kuna lafiya kuma a ko da yaushe dai muna jin dadin shirye-shiyenku. Dalilin wannan wasika shi ne domin ku bayyana mana mu masu sauraro cewar mene ne dalilin da ya sa sojojin ruwan kasar Japan suka kama jirgin ruwan kama kifi na kasar Sin, kuma har suka tsare kaftin din jirgin?"

To, malama Fatima, mun gode. Lallai kina mai da hankali kan harkokin da suke faruwa dangane da kasar Sin sosai. Yanzu Japan ta riga ta saki kyaptin din jirgin ruwan kama kifaye da ta tsare a kwanakin baya. Kuma ya zuwa ya komo gida. A matsayinmu Sinawa, muna fatan Japan za ta daidaita wannan lamari yadda ya kamata, a kokarin bunkasa dangantakar abokantaka tsakaninta da kasar Sin.

Sakon malama Fatima ke nan. Bayan haka, malam Samaila Zagga a jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Babu shakka bikin EXPO na Shanghai, wato bikin baje kolin duniya da ake yi a birnin Shanghai na kasar Sin, wanda zai kammala nan ba da dadewa ba. Hakika ya samu nasarori da dama. Daya daga cikinsu shi ne na fannin diplomasiyar dake tsakanin kasashe da al'ummominsu da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa a fannonin fasahohin ci gaban zamani. Ina fatan Allah ya sa a kammala wannan biki cikin nasara, amin."

To, mun gode, malam Samaila Zagga. A hakika dai, muna alfahari sosai da samun damar gudanar da bikin baje kolin duniya a birnin Shanghai na Sin. Bisa wannan dama, mun gwada karfinmu a fannonin tattalin arziki, cinikayya, zamantakewar al'umma da dai sauransu. Bugu da kari, mu ma mun samu ci gaba a wadannan fannoni. Dadin dadawa, mu Sinawa muna son baki kwarai da gaske. Mun yi farin ciki sosai da abokanmu suka kawo ziyara a kasar Sin daga wurare daban daban na duniya baki daya. Da fatan za mu kara yin mu'amala tare da juna a nan gaba. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Bayan haka, sauran masu sauraronmu da yawa sun aiko mana da wasiku, kamar malam Alhaji Wushishi Danlami a tarayyar Nijeriya, da malam Issa Musa a Kamaru, da malam Madina Adamou a Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba, sabo da karancin lokaci. Don haka muna farin ciki da sakwannin naku. Da fatan za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu na Amsoshin Wasikunku. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China