in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da ranar rumfar kasar Morocco a bikin EXPO na Shanghai
2010-09-30 15:47:24 cri

Yau Alhamis 30 ga wata, an kaddamar da ranar rumfar kasar Morocco a bikin EXPO na Shanghai. Shugaban majalisar wakilai na kasar Morocco Abdelwahed Radi da direktan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar birnin Shanghai Liu Yungeng sun halarci bikin tare da ba da jawabi.

Abdelwahed Radi ya nuna cewa, halartar kasar Morocco a wannan biki ya alamanta cewa, dangantakar sada zumunci tsakanin kasashen biyu ta sami sabuwar bunkasuwa. Ta hanyar duba rumfar kasar Morocco an iya fahimtar yadda kasar ta mai da babban muhimmanci kan bikin, da fasahar gine-ginen kasar da kuma al'adun kasar. Ban da wannan kuma, ya ce, gobe rana ce ta cika shekaru 61 da kafuwar sabuwar kasar Sin, a wannan lokaci, sarkin kasar yana sa ran alheri ga kasashen biyu domin su kara inganta dangantakar dake tsakaninsu.

Liu Yungeng ya bayyana cewa, Morocco ita ce kasa daya tak daga cikin kasashen Afrika da ta gina rumfarta da kanta. Yana fatan kasashen biyu sun kara raya dangantakar sada zumunci dake tsakaninsu ta hanyar wannan bikin.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China