in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana maraba da ranar rumfar kasar Sin a bikin EXPO
2010-09-29 22:01:04 cri

Ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta bikin murnar kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, wadda kuma za ta kasance ranar rumfar kasar Sin a wajen bikin EXPO na Shanghai. Ranar 29 ga wata da maraice, an shirya taron manema labarai a cibiyar bikin EXPO na Shanghai, inda shugabannin rumfar kasar Sin, gami da mataimakin shugaban hukumar daidaita harkokin bikin EXPO na Shanghai suka halarci taron, da gabatar da ayyukan da za a shirya a yayin ranar rumfar kasar Sin.

Bikin baje-kolin kasa da kasa da ake gudanar a birnin Shanghai na kasar Sin a shekara ta 2010, wani kasaitaccen biki ne wanda ke inganta mu'amala tsakanin jama'ar kasashen duniya daban-daban. A matsayin dakin nune-nune na kasa masaukin bikin EXPO, rumfar kasar Sin ta dade tana jawo hankalin jama'a.

Rumfar kasar Sin tana mayar da hankali kan nuna nagartattun al'adun kasar, da bayyana babban take na "hikimomin al'ummar kasar Sin yayin da ake bunkasa birane". A nasa bangaren, shugaban rumfar bikin EXPO na Shanghai Mista Xu Hubin ya ce:

"Ba ma kawai salon ginin rumfar kasar Sin ba, har ma abubuwan da ake nunawa a ciki, dukkansu sun bayyana irin haduwar dake tsakanin fasahohin zamani da hazikancin gargajiya na al'ummar kasar Sin, wadanda ke samun babban yabo daga baki na gida da na waje, da masana daga bangarori daban-daban, gami da 'yan kallo na gida da na waje."

Mista Xu Hubin ya bayyana cewa, kawo yanzu, rumfar kasar Sin ta kammala aikin kaddamar da bikin EXPO na Shanghai, da bikin bude farfajiyar EXPO, da sauran ayyuka tare da cikakkiyar nasara, haka kuma ta nuna kwazo wajen yin mu'amala da cudanya tare da sauran dakunan nune-nune, da kara samun fahimtar juna da inganta hadin-gwiwa tare da mahalarta bikin daga sassa daban-daban na duniya.

Bisa labarin da muka samu, an ce, bisa ga la'akari da sauyawar yanayi da adadin 'yan kallo, za a ci gaba da kyautata hidimomin da ake bayarwa, da samar da wani kyakkyawan muhalli ga 'yan kallo. Mataimakin shugaban rumfar kasar Sin Mista Qian Zhiguang ya bayyana cewa:

"Domin bada tabbaci ga bin doka da oda a rumfar kasar Sin, da kara biyan bukatun 'yan kallo da yawansu ke ci gaba da karuwa, ana kokarin kiyayewa da yin gyare-gyare ga na'urorin da ake amfani da su a rumfar kasar Sin. A lokacin da aka gamu da wata matsala, za a kaddamar da wata hanya ta musamman ba tare da bata lokaci ba, domin kwashe mutanen da suka yi cincirindo."

Ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 61 da kafa sabuwar kasar Sin, kana za a taya murnar ranar rumfar kasar Sin a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai. Shugabannin kasar Sin da sauran manyan baki daga gida da waje za su halarci bikin. A nasa bangaren kuma, mataimakin shugaban rumfar kasar Sin Mista Qian Zhiguang ya ce, ana nan ana yin kokarin da ya dace wajen tabbatar da shirya bikin ranar rumfar kasar Sin yadda ya kamata:

"Yanzu, domin bada tabbaci ga shirya ayyuka daban-daban yadda ya kamata a ranar rumfar kasar Sin, dukkanin ma'aikatan wurin suna zage damtse wajen kyautata ayyuka a fannoni daban-daban, a kokarin bayar da kyakkyawar hidima ga manyan baki da sauran 'yan kallo."(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China