in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da ranar rumfar kasar Libya na bikin EXPO na Shanghai
2010-09-29 16:39:54 cri

Yau Laraba 29 ga wata da safe, an kaddamar da ranar rumfar kasar Libya na bikin EXPO na Shanghai. Shugaban hukumar ba da sadaka da samun bunkasuwa ta Gaddafi GICDF Mr Saif Islam Gaddafi, da mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Zhaijun sun halarci bikin tare da ba da jawabi. Jakadan kasar Libya dake nan kasar Sin Mr Taher E.A. Jehaimi, da mataimakin babban wakilin gwamnatin kasar Sin Li Zhiguo da sauransu sun halarci bikin.

Saif Islam Gaddafi ya yi jawabi cewa, bikin a wanna karo muhimmin biki ne na kasa da kasa.

A cikin jawabin da ya yi, Zhaijun ya nuna cewa, kasashen Sin da Libya suna da zumuncin gargajiya mai karfi, kuma ya yi imani cewa, bikin a wannan karo ya samar da zarafi mai kyau wajen bunkasa dangantakar sada zumunci dake tsakain kasashen biyu.

A gun bikin, 'yan wasan fasaha daga kasar Libya sun yi wasanni tare da samun karbuwa da dama.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China