in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jimillar ciniki a tsakanin Sin da Afirka ta karu yadda ya kamata
2010-09-28 14:31:47 cri
Sakamakon illar da matsalar kudi ta duniya ta haifar, jimillar ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta ragu a shekara ta 2009 bayan da ta samu saurin karuwa a jerin shekaru 8. Taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a karshen shekara ta 2009 ya sake farfado da hadin kan bangarorin biyu ta fuskar cinikayya, kana kyautatuwar yanayin tattalin arziki da cinikayya na duniya ta aza harsashi ga karuwar jimillar ciniki a tsakanin Sin da Afirka. Bisa sabon rahoton kididdiga da bankin raya Afirka ya bayar a wannan wata, an ce, jimillar ciniki a tsakanin Sin da Afirka ta sake dagawa a fannoni daban daban.

Wannan rahoto mai taken "ciniki da ayyukan zuba jari da kasar Sin ta yi a Afirka" ya nuna cewa, bayan jimillar ciniki a tsakanin Sin da Afirka ta zarce dala biliyan 100 a shekara ta 2008 a karo na farko, kasar Sin ta zama kawar Afirka ta farko ta fuskar cinikayya a shekara ta 2009.

A waje daya kuma, kasar Sin tana ta kara zuba jari ga kasashen Afirka, wanda ya shafi ayyuka fiye da 4000, yawan masana'antun kasar Sin da suka zuba jari a Afirka ya kai kimanin 2000, wadanda suke gudanar da ayyukansu a fannonin ayyukan gona da ma'adinai da ayyukan sarrafawa da muhimman ayyukan yau da kullum kana da tafiyar da cinikayya.

Leonce Ndikumana, shugaban sashen binciken kasuwanni na bankin raya Afirka ya bayyana cewa, sakamakon kara bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da kuma karuwar bukatun da aka yi a gida, yawan kayayyakin da Afirka kan fitar zuwa kasar Sin yana ta karuwa, wanda ba kawai ya samar da babbar kasuwa ga kayayyakin Afirka ba, hatta ma ya samar da wata dama da kuma kalubale ga sana'ar shigar da ta fitar da kaya zuwa ketare ta Afirka wajen yin takara a duniya.

Abin da ya kamata a lura shi ne, domin kara bude kasuwa ga kayayyakin Afirka da kuma sa kaimi ga shigo da kayayyakin Afirka cikin kasar Sin, a watan Yuli na bana, kasar Sin ta tsai da kudurin soke harajin kwastam ga kayayyakin da yawansu ya kai kashi 60 cikin kashi dari da kasar Sin ke shigowa da su daga kasashen Afirka 26 da suka fi fama da talauci. Ban da wannan kuma, a cikin shekaru 3 masu zuwa, sannu a hankali, gwamnatin kasar Sin za ta soke harajin kwastam ga kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen Afirka da yawansu ya kai kashi 95 cikin kashi dari, wadanda suke fama da talauci mai tsanani kuma suke da huldar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar.

Ban da karuwar yawan kudin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasar Sin, a shekarun nan, ire-iren wadannan kayayyaki suna ta sauyawa. Rahoton ya nuna cewa, kawo yanzu, kayayyakin da yawansu ya kai kashi 70 cikin kashi dari da kasar Sin kan shigo da su daga Afirka su ne gurbataccen man fetur da amfanin gona. Haka kuma yawan kayayyakin da suka shafi al'adu da yawon shakatawa da Afirka kan aika da su zuwa kasar Sin ya fara karuwa. A cikin kayayyakin da kasar Sin ta kan aika da su zuwa Afirka, kashi 38 cikin kashi dari na'urori ne a fannonin samarwa da zirga-zirga, wadanda suka ba da tabbaci sosai ga kasar Sin wajen tallafawa Afirka ta fuskar raya muhimman ayyukan yau da kullum.

Mtuhli Ncube, masanin tattalin arziki na bankin raya Afirka ya nuna cewa, daga kayayyakin gida ko na sassaka zuwa na'urori manya ko kananan, dukkansu da kasar Sin ke samarwa suna da inganci da kuma araha, wadanda ke iya biyan bukatun masana'antu da masu sayayya na Afirka sosai, hakan ya aza harsashi ga bunkasuwar tattalin arzikin Afirka.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China