A cikin jawabin fatan alheri da Mr. Zhou Bohua ya yi, ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan, a karkashin kokarin bangarorin biyu, dangantakar kasashen biyu ta kara bunkasa cikin hanzari, kuma hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya da ke tsakaninsu ta samu sakamako mai gamsarwa. Yana fata za a yi amfani da bikin Expo na Shanghai, domin kara fahimtar juna da koyon fasahohi da sada zumunci da ke tsakaninsu, don kara inganta dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci da ke tsakaninsu.
Emilie Beatrice Epaye ta yi jawabin fatan alheri, inda ta bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan, kasar Afrika ta tsakiya na yin gyare-gyare da dama, kuma tana fatan yin amfani da wadannan gyare-gyare don kawo wani kyakkyawan muhallin zuba jari ga masu zuba jari na kasashen waje, haka kuma, kasar Afrika ta tsakiya za ta yi amfani da bikin Expo na Shanghai, don inganta hadin gwiwa da ke tsakaninta da kasar Sin, da inganta dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci da ke tsakaninsu.(Bako)