in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayan kamfanin kera motoci na Geely ya sayi kamfanin Volvo
2010-09-20 16:37:30 cri
Garba: A watan Maris na bana, kamfanin kera motoci kirar Geely na kasar Sin da kamfanin Volvo na kasar Sweden sun kulla wata kwangilar da darajarta ta kai dalar Amurka biliyan 1.8 a hedkwatar kamfanin Volvo da ke kasar Sweden. Bisa wannan kwangila, kamfanin Geely ya sayi dukkan takardun hannun jari na kamfanin Volvo.

Sanusi: bayan watanni 6 da suka gabata, a kwanan nan, kamfanin Geely ya sanar da cewa, yawan motocin da ya sayar a cikin wannan lokaci ya kai dubu 190, wato ya karu da kashi 42 cikin dari. Kana kuma yawan ribar da kamfanin ya samu ya kai kudin Sin RMB yuan miliyan dari 8, wato ya karu da kashi 35 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na bara.

Garba: A hakika dai, wannan wani mataki ne na farko da kamfanin Geely yake kokarin dauka don zama wani shahararen kamfanin kera motoci na duniya bayan da ya sayi kamfanin Volvo. Bisa shirin da Mr. Li Shufu, shugaban hukumar direktocin kamfanin Geely ya tsara, kamfaninsa ya sayi kamfanin Volvo ne domin mallakar tambari da fasahohin zamani na kamfanin Volvo. Mr. Li Xiaofei, mataimakin babban edita na wata mujellar kera motoci da wasannin motsa jiki ya yi nazari cewa, "Bisa yawan kudin da ya kashe, kamfanin Geely na kasar Sin ya sayi kamfanin Volvo baki daya. A 'yan shekarun da suka gabata, kamfanin Ford ya kashe kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 6.4, amma a wannan karo, kamfanini Geely ya kashe kusan dalar Amurka biliyan 2 kawai. Ko da yake yawan kudin da kamfanin Geely ya kashe ya yi kadan idan an kwatanta shi da na kamfanin Ford, amma lokacin da kamfanonin kasar Sin suke kokarin yin gasa a kasuwannin kasashen duniya, ya kamata mu mai da hankali kan moriyar da wannan kamfanin samar da motoci yake iya samu bayan da ya sayi wani jarin kamfanin waje."

Sanusi: Bisa kwangilar da kamfanin Geely na kasar Sin ya kulla da kamfanin Volvo, za mu iya gano cewa, kamfanin Geely zai ci gaba da yin amfani da farfajiyoyin masana'antun kamfanonin Volvo da ke kasashen Sweden da Belgium, kuma zai gina sabuwar farfajiyar masana'antar kera mota kirar Volvo a kasar Sin domin samar da motocin kirar Volvo da ke biyan bukatun da ake da su a kasar Sin. Bugu da kari, kamfanin Geely zai ci gaba da tabbatar da kyakkyawar huldar da ke tsakaninsa da ma'aikata da kungiyar kwadago da 'yan kasuwa wadanda suke samar da kayayyaki ga kamfanin Volvo da wadanda suke sayar da motoci kirar Volvo. Mr. Li Xiaofei ya nuna yabo cewa, "Bisa shirin sayen kamfanin Volvo da kamfanin Geely ya tsara, an ce, abin da Mr. Li Shufu, shugaban hukumar direktocin kamfanin Geely yake nazari shi ne yana son lakanta da kuma mallakar fasahohin zamani na aiwatar da wani kamfanin kera motoci daga wajen kamfanin Volvo wanda ke da dogon tarihin kera motoci masu inganci da tambarin da ya yi suna a duk duniya."

Garba: A kwanan nan, an dauka cewa, mai yiyuwa ne kamfanin Geely zai gina sabuwar farfajiyar masana'antar kera motoci kirar Volvo ko a birnin Beijing, ko a birnin Chengdu, ko a birnin Tianjin, ko kuma a birnin Shanghai, amma a hakika dai, har yanzu ba a tabbatar da wurin da za a kafa wannan farfajiya ba tukuna.

Sanusi: A 'yan shekarun nan, masana'antun kera motoci na kasar Sin sun samu ci gaba sosai, har ma kasar Sin ta zama kasuwar motoci mafi girma a duniya a shekarar 2009. Amma har yanzu kamfanin Geely yana fuskantar matsaloli iri iri bayan da ya sayi kamfanin kera motoci na Volvo. Da farko dai, ba shi da fasahar sayar da motocinsa a kasuwannin ketare, sannan kamfanin Geely ba shi da fasahar kera motoci masu inganci kuma masu tsada. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, yawan hasarar da kamfanin Volvo ya kan yi a kowace shekara ya kai dalar Amurka biliyan 1. Mr. Li Xiaofei ya kara da cewa, "Kalubale mafi tsanani da kamfanin Geely ke fuskanta yanzu shi ne yaya zai iya fitar da kamfanin Volvo daga mawuyacin hali da ya shiga domin yana bukatar fahimtar al'adu da yadda kamfanin Volvo ya sanya gabansa, har ma yana bukatar shiga aikin kyautata tunani da shirin sayar da motocin da na kamfanin Volvo ya kera."

Garba: Haka kuma, wannan cinikin da aka yi a tsakanin kamfain Geely da na Volvo zai taimakawa sauran kamfanonin kera motoci na kasar Sin wajen gyara aikinsu. Mr. Li Xiaofei ya kara da cewa, "Wannan cinikin da aka yi a tsakanin kamfanin Geely da na Volvo ya zama wani sabon batu ga sauran kamfanonin kera motoci na kasar Sin da na kasashen waje, kuma an gano wata sabuwar hanya. Yanzu motocin da kamfanonin kasar Sin suke samarwa sun fi yawa a duniya. Ba ma kawai suna bukatar sayar da motocinsu a kasuwar cikin gida ba, har ma suna bukatar sayar da su a kasuwannin ketare." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China