in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Murnar bikin haduwar iyali na kasar Sin
2010-09-20 13:50:37 cri
Masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Ko kun san cewa, ran 22 ga watan Satumba rana ce ta bikin haduwar iyali na kasar Sin. A wannan rana, membobin iyali su kan hadu a gu daya domin murnar wannan rana. Game da asalin bikin haduwar iyali kuma, akwai tatsuniyoyi da dama a tarihin kasar Sin da suke bayyana asalin wannan rana. Daya daga cikinsu na da alaka da wata mace mai suna Chang E, wadda ta tafi zuwa duniyar wata bayan shan wani irin magani.

A zamanin da da can, wata rana, rana guda 10 sun fito a sararin samaniya. Alamarin da ya haddasa zafi sosai. Har ma ruwan teku ya kafe. Sannan jama'a ma ba su iya ci gaba da rayuwa ba.

Wannan lamarin ya girgiza wani jarumi mai suna Hou Yi, wanda ya hau babban dutse Kunlun har zuwa kolinsa, ya harbo rana 9 ta hanyar amfani da kwari da baka.

A sakamakon haka, Hou Yi ta ba da gudummawa sosai. Wannan ya sa ya samu karbuwa daga jama'a kwarai da gaske. Mutane da yawa sun zo wurinsa a kokarin koyon fasahohi. Daya dga cikinsu shi ne wani mai wayo sosai mai suna Peng Meng.

Ba da dadewa ba, Hou Yi ya yi aure da wata mace mai suna Chang E, wadda take da kyan gani sosai. Daga bisani, ban da koyar da dalibai da yin farauta, Hou Yi ya kan zauna tare da matarsa. Mutane da dama sun nuna masa hassada.

Wata rana, Hou Yi ya kai ziyara a gidan wani abokinsa dake babban dutsen Kunlun. A kan hanyarsa, sai ya gamu da matar Ubangijin Wangmu, inda ya samu wani maganin hana mutuwa daga wajenta. Wai idan aka sha rabin maganin, to mutum ba zai mutu ba har abada. Kuma idan aka sha maganin duka, mutum zai zama Ubangiji nan take.

Duk da haka, Hou Yi ba ya son yin ban kwana da matarsa. Sai ya bar maganin a wajen Chang E. Amma Peng Meng mai wayo sosai ya samu wannan labari.

Bayan kwanaki uku, sai Peng Meng ya yi wa Hou Yi karya cewa, ba shi da lafiya. Bayan da Hou Yi ya je farauta tare da dalibai duka, sai Meng Peng ya ruga cikin dakin Chang E tare da wani takobi. Ya yi mata barazana da ta bayar da maganin. In ba haka ba, zai kashe ta. A daidai wannan lokaci, Chang E ta yanke shawara, ta dauki maganin ta sha nan take.

Bayan haka, sai jikin Chang E ya tashi, ya fito daga taga zuwa samaniya. Amma sabo da Chang E ta damu da mijinta Hou Yi, sai ta je duniyar wata da ta fi kusa da kasa, ta zama Ubangiji a can.

Bayan da ya koma gida da dare, sai aka gaya wa Hou Yi abin da ya faru. Ya ji mamaki kwarai da gaske, kuma ya yi fushi sosai. don haka ya nemi ya kashe Peng Meng, amma ya riga ya tsere. Hou Yi ya yi kuka, ya kira sunan matarsa Chang E ta fuskar duniyar wata. A daidai wannan lokaci, ya tarar da cewa, duniyar wata a yau ta fi yin haske. A ciki kuma, akwai wata mace da ta yi kama da Chang E sosai.

Bayan da mutane suka samu wannan labari, su kan yi addu'a ta fuskar duniyar wata. Daga bisani, a kan sheda duniyar wata a ranar bikin haduwar iyali na kasar Sin.

To, jama'a masu sauraro, ko kun gamsu da wannan tatsuniya dangane da bikin haduwar iyali na kasar Sin? A daidai wannan lokaci kuma, muna fatan dukkanku za ku samu zaman lafiya, kwanciyar hankali, nishadi da wadata. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Bayan haka, a kwanan baya, malam Musa Tijjani Ahmad a Kano, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Hakika na yi matukar farin ciki da samun nasarar wannan gagarumin gasar kacici-kacici kan lardin Sichuan, wanda nake fatan kai ziyarar gani-da-ido idan Allah ya yarda. Sannan na ga sunana amma ban ga wani karin bayani ba a kan wadanda suka sami lambobin yabo, wanda ina daya daga cikinsu. Sannan a Shekara ta 2008, kun shirya wata gasa makamanciyar wannan wanda na samu lambar yabo na zuwa Sin amma shiru kake ji kamar an shuka dusa."

To, malam Ahmed, a hakika dai, ba duk wanda ya samu lambar yabo a gasar kacici-kacici zai samu damar kawo ziyara a kasar Sin ba. Yanzu gidan rediyon CRI yana gabatar da shirye-shirye da harsuna 53. A sabili da haka, kila bana masu sauraro da suka samu lambar yabo na harshen Hausa suna iya kawo ziyara kasar Sin, yayin da badi masu sauraron na sauran harsuna za su kawo ziyara kasar Sin. Duk da haka, mun yi imani cewa, ba za ka rasa dama ba idan ka ci gaba da kokari kamar yadda ka yi a da. Allah ya taimake mu, amin.

Sakon malam Ahmed ke nan. Bayan haka, malama Zainan Musa Gwadabawa, matar shugaba Bello Abubakar Malam Gero a Nijeriya, ta bayyana mana cewa, "Ina mai matukar jin dadin da kuka samu sakona. In mai sanar da ku cewa, dalilin rashin samun sakona cikin dogon lokaci shi ne, ina makaranta ina ci gaba da karatuna domin mijina ya samanmin karatu a jami'ar usmanu dan fodiyo dake Sokoto. Ina karatun digiri harshen Larabci, wato arabic. A halin yanzu, ina shekara ta 2, zan shiga 300lb wato uj 3 kenan. Bayan haka, a ko da yaushe ina sauraron shirye-shiryenku na maraice da kuma na safe. Ko da yake yanzu muna nan gida domin an samu ambaliyar ruwa a Sokoto, inda hanyoyi da gadoji da dama sun kare, wato kamar hanyar Sokoto zuwa Kware, da Sokoto zuwa jami'ar da dai makamantansu. abubuwa dukka sun tsaya cik a jami'a a sanadiyar wannan ambaliyar ruwa. Don haka yanzu muna gida muna jiran tsammani idan an yi hanyoyin wucin gadi. To, muna sa ran za a koma bakin karatu. Daga karshe, ina godiya ga CRI hausa domin kulawa da ni. Na gode."

To, malama Zainan, mun yi farin ciki sosai da samun sako daga wajenki, Allah kuma ya mayar da alheri sakamakon gamuwa da bala'in ambaliyar ruwa a Sokoto. Muna fatan za ki ci gaba da mai da hankali a kan shirye-shiryenmu, da fatan za ki samu karatu a jami'ar yadda ya kamata. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China