Lardin Qinghai yana kan tudun Qingzang, inda ake iya samun kyan surar tudu da manyan duwatsu da kyawawan tabkoki da makeken filin ciyayi kana da hamada mai girma. La Haiqing, musulmi dan kasuwa da ya shahara sosai a wurin ya bayyana cewa, ya nuna kauna sosai ga wannan kyakkyawan wuri, musamman ma al'adunsa.
"yayin da nake kasuwanci, na kan nemi samun ilmin da nake so in sani. Daga baya kuma na gano cewa, ana iya samun al'adu iri daban daban a garina."
Bisa kwazon da ya nuna, La Haiqing ya kafa wani wurin nuna duwatsu masu ban mamaki da ke kama da wasu halittu a gudumar Guide ta lardin Qinghai. A cikin wannan wurin da fadinsa ya zarce murabba'in mita dubu 30, ana iya gano dubban manyan duwatsu masu ban mamaki da ke kama da siffar mutum ko kayayyaki, wasu kuwa sun zama tamkar zane-zanen da ke da launuka iri daban daban. La Haiqing ya gaya wa wakiliyarmu cewa, wadannan siffofi da launuka halitta ce ta bayar a maimakon dan Adam. Sakamakon kasancewar manyan duwatsu da kwazazzabo a gundumar Guide, ana iya samun dimbin duwatsu masu ban mamaki da ke kama da wasu halittu. Yayin da yake tabo magana kan yadda ya gano wadannan duwatsu, La Haiqing ya yi murmushi ya bayyana cewa,
"yayin da nake gudanar da aikin gine-gine, na gina dakunan kwana a cikin farfajiyar gidanmu, kuma na sayi duwatsu da yawa domin kayatar da farfajiyar. Sannu a hankali na gano cewa, duwatsun na da kyan gani sosai, don haka na fara nuna sha'awa kan su. A idona, inda an ajiye su a cikin farfajiya, to za su zama tamkar kayayyakin fasaha. Sabo da haka na nuna kauna sosai gare su."
Kawo yanzu, La Haiqing ya riga ya kebe kudade kusan Yuan miliyan 8 wajen habaka wurin nuna duwatsu masu ban mamaki da ke kama da wasu halittu, wanda ya jawo hankulan masu yawon shakatawa na kasa da kasa, ta haka ya zama tamkar wani tauraro a fannin sha'anin yawon shakatawa na wurin, La Haiqing kuwa ya yi suna sosai a gundumar Guide.
Yayin da mutane suka gano nasarar da La Haiqing ya samu, kakilan ne sun san cewa, lallai ya sha wahalhalu sosai a farkon lokacin da yake raya aikinsa. La Haiqing mai shekaru 47 da haihuwa, an haife shi ne a cikin wani karamin kauye da ke da wuyar zuwa na gundumar Guide, manyan duwatsun da ke gaban gidansa sun zama wurin nishadi a lokacin yarintarsa. Don haka tun yana yaro, yake nuna kauna sosai ga garinsa. Bayan da ya gama karatu daga jami'a, La Haiqing ya samu gurbin aikin yi a cikin gwamnatin gundumar. Amma sakamakon jawabin da tsohon shugaban kasar Sin Deng Xiaoping ya yi a shekara ta 1992 kan bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, ba wata wata ya bar aikinsa da kuma fara yin kasuwanci. Yayin da yake tuna da kudurin da ya tsayar a wancan lokaci, La Haiqing ya furta cewa,
"A wancan lokaci, wasu mutane ba su fahimce ni ba, ni ma ban tabbatar da cewa, ko wannan kuduri ya yi daidai ko bai yi daidai ba. Amma na yi niyyar cewa, dole ne na yi kasuwanci, ko da yake kila zan ci tura. Na yi imanin cewa, kasar Sin ta riga ta kama hanyar samun bunkasuwa a fannoni daban daban, zamanin samun wadata yana zuwa."
A shekarar bara, an bude wurin shan iska na yanayin kasa na kasar Sin a gundumar Guide da La Haiqing ya kebe kudade Yuan miliyan 86 wajen raya shi. La Haiqing ya gaya wa wakiliyarmu cewa, ana iya samun wani irin yanayin kasa na musamman da ke da launin ja a gundumar Guide, kuma wurin ya samar da wata irin laka da ke da launuka iri 7, don haka ya gina wannan wurin shan iska ne domin gabatar da kyan surar garinsa ga dimbin mutane. Laka tushe ne na kasancewar bil Adam, ya kamata kowa ya san ta da kuma lura da ita. La Haiqing ya kara da cewa,
"A ganina, kasa ta iya nuna farin ciki ko bakin ciki, amma mu bil Adam ba mu taba kulawa da abubuwan da ta ji a rai ba, ko da mun dade muna zaman rayuwa a kan doronta daga zuriya zuwa zuriya. Ina fatan zan iya zama mutumin farko da ke iya gano abubuwan da kasa ke ji. Na sayar da lakar da ke da launuka iri 7 ga ko wane Basine ko Basiniya, tare da fatan kowa ya iya gano cewa, laka abu ne mai daraja sosai a duniya, ya kamata bil Adam mu lura da ita kwarai da gaske."
Kyan karkarar wurin shan iska na yanayin kasa na Guide ya shaku cikin zukatan masu yawon shakatawa, bayanin da La Haiqing ya yi kuwa ya burge ko wanensu. Mr. Ozgur daga kasar Turkiya ya nuna babban yabo ga wurin, cewar
"duwatsu masu ban mamaki da ke kama da wasu halittu da wurin shan iska na gundumar suna da ban sha'awa sosai. Mr. La kuwa mutum ne mai fara'a. Ya kebe kudade masu dimbin yawa ba don cin riba ba sai dai domin sha'awar da ya nuna wa muhallin halittu da yanayin kasa na wurin. Lallai wurin na iya jawo hankalin mutane sosai. A ganina, idan mutane sun je Qinghai, amma ba su isa wannan wurin shan iska ba, to babu shakka zai zama wani abin bakin ciki sosai."
Kokarin da La Haiqing ya yi ya ba da gudummowa sosai ga bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa da na al'adu na gundumar Guide, don haka ya samu goyon baya daga wajen gwamnatin wurin. Ma Jinxing, ministan watsa labarai na gundumar ya bayyana cewa,
"yayin da La Haiqing ya raya aikin nuna duwatsu masu ban mamaki da ke kama da wasu halittu da wurin shan iska na yanayin kasa, gwamnatinmu ta taimaka masa a wasu fannoni da kudade kana da ma'aikata. A nan gaba, za mu shigo da wasu gagaruman harkokin al'adu cikin wannan wurin shan iska, tare da fatan za a iya kara samun bunkasuwa bisa goyon bayan da kasarmu ke nuna wa sha'anin al'adu."
Yanzu La Haiqing yana tattara laka mai launuka iri 7 da ke tudun Qingzang, da fatan cewa, a cikin shekaru da dama masu zuwa, zai iya gabatar da irin wannan lakar da ya gano ga duk fadin kasar Sin har ma ga duniya baki daya, ta yadda za a iya gano al'adun duwatsu da laka na tudun Qingzang na kasar Sin.(Kande Gao)