Kwararru da masana da 'yan kasuwa fiye da dari daya da suka fito daga kasashen Faransa da Sin da kasashen Afrika sun halarci wannan taro. Darektan ofishin nazarin bunkasuwa na bankin raya Afrika na ganin cewa, nahiyar Afrika tana fuskantar gyare-gyare da yawa, ya kamata kasashen Afrika su kara yin kokarin raya tattalin arziki amma ba kubutar da kangin talauci kawai ba, sabo da haka, kasashen Afrika suna bukatar kawa kamar kasar Sin. Ya ce, "kasar Sin ta zuba jari a kasashen Afrika, kana kasar Sin ta nuna kwarewa wajen raya tattalin arziki, hadin gwiwa a tsakaninsu ya kawo moriyar juna."