Shugaban kamfani mai suna "Ke Duo Wei" na birnin Shenzhen Hui Honglin yana daya daga cikin shugabannin matsakaita da kananan kamfanonin kasar Sin da ke yin ciniki tare da kamfanonin kasashen Afirka. A shekarar 2001, Hui Honglin tare da abokansa sun tara kudin Sin RMB miliyan daya, kuma sun kafa kamfani kansu, wannan kanfani yana kula da harkokin fitar da kayayyakin sake-sake zuwa kasashen Afirka. Amma kamfanin ya taba fuskantar kalubale da yawa.Hui Honglin ya bayyana cewa: "muhimmin kalubalen da muke fuskantar shi ne rashin kudi, kuma a ganina akwai wuya ga kasar da ta nuna goyon baya ga kananan kamfanoni."