To, mun gode, malam Gargajiga, mai sauraronmu a kullum. Lallai kana mai da hankali kan shirye-shiryenmu na CRI cikin dogon lokaci, tare da ba da shawarwari masu kyau. To, game da tambayoyin da ka yi a cikin wannan sako, za mu ba da amsa bisa iyakacin kokari. Ban da malam Abubakar dan kabilar Hui, mafi yawanmu ma'aikatan Hausa Sinawa 'yan kabilar Han. Kuma mun zo ne daga wurare daban daban na kasar Sin, kamar Daqing, Changsha, Zhengzhou, Wuhan da dai sauransu. Bayan haka, dukkanmu mun zo ne daga jami'o'i guda biyu, wato jami'ar koyon harsunan waje ta birnin Beijing, da jami'ar koyon ilmin yada labarai ta kasar Sin. Muna fatan malam Gargajiga da sauran membobin club din za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.
Sakon malam Gargajiga ke nan. Bayan haka, shugaban kungiyar masu sauraron rediyon kasar Sin ta jihar Sokoto, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Ina mai amfani da wannan dama ne domin in isar da sakon juyayi ga al'ummar kasar Sin tare da ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin dangane da irin bala'in ambaliyar ruwa da ta ci wasu sassa na kasar Sin. A madadi na ni shugaba da sakataren kungiya Aliyu Filasko Bakaniken Mota More da dukkan membobin kungiyar muna taya ku juyayin wannan musiba, da fatan Allah ya tsare gaba, amin."
To, mun gode, shugaban kungiyar masu sauraronmu ta jihar Sokoto, tarayyar Nijeriya. Sai dai muna fatan a gaba za ka bayyana mana sunanka, kuma dukkanmu Sinawa za mu yi iyakacin kokari domin cimma nasarar fama da bala'in. Da fatan duk wadanda suke fama da bala'in za su samu damar farfado da zaman rayuwarsu cikin sauri. Allah ya taimake mu, amin.
A kwanan baya, malam Abdullahi Garba a Kano, tarayyar Nijeriya ya yi tambayar cewa, "Don Allah ko za ku ba da wani bayani kan dandalin tattaunawar Davos?" To, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya, da fatan malam Abdullahi kana sauraronmu.
Za a kaddamar da dandalin tattaunawar Davos na yanayin zafi a shekarar 2010 a ran 12 ga watan Satumba a birnin Tianjin na kasar Sin, wanda yake daukar nauyin shiryawa bisa gwargwadon karfinsa na tattalin arziki dake bunkasa a yau da kullum. Birnin Tianjin ya riga ya share fage a fannonin dakin taron, tsugunar da jama'a, zirga-zirga, tsaro da dai sauransu.
A game da birnin Tianjin, wannan ne karo na biyu da za a kaddamar da dandalin tattaunawar Davos a wannan wuri. A sabili da haka, ya saba da irinsa sosai. Tianjin yana share fage yadda ya kamata. Magajin garin birnin Tianjin Huang Xingguo ya bayyana cewa, za a kara ba da mamaki ga mahalarta na kasar Sin da na ketare, a kokarin shaidawa duniya wani birnin Tianjin mai cike da kuzari.
Babban sakataren kwamitin shirya dandalin tattaunawar Davos a wannan karo Zhu Jun ya bayyana cewa,
"Za mu zabi mazaunan birnin Tianjin guda biyar domin halartar dandalin tattaunawar, a kokarin kara fahimtarsu ga Davos. Wannan ne karo na farko a cikin shekaru 40 da suka gabata."
Za a kafa babban dakin taron Davos a cibiyar baje kolin Meijiang, inda ake dab da kammala dukkan ayyukan karbar bikin. Babban dakin taron yana iya daukar mutane 1500. Liu Changjin, jami'in kula da aikin kafa cibiyar ya bayyana cewa,
"Wannan daki zai kasance wani dakin addu'a. Sabo da mahalarta taron suna bin addinai daban daban, shi ya sa an yi la'akari da bukatunsu yadda ya kamata."
A yayin shirya dakin taron, a kokarin bayyana makasudin dandalin tattaunawar Davos a wannan karo na "Kiyaye muhallin halittu da yin tsimi", da takensa na "Sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa", gwamnatin birnin Tianjin ta gabatar da shirye-shiryen kiyaye muhalli guda 20 wajen gudanar da taron, wadanda suka shafi fannoni 7, kamar dakunan taron, zirga-zirga da dai sauransu, a kokarin rage fitar da gurbataccen iska da yin tsimin makamashi daga duk fannoni.
A cikin 'yan shekarun da suka gabata, Tianjin tana bunkasa cikin sauri, musamman ma sabon yankin Binhai. Ban da yankin Shenzhen na musamman a fannin tattalin arziki da sabon yankin Pudong na birnin Shanghai, Tianjing ta kasance wani sabon yanki dake jagorantar bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin. An yi imani cewa, wadanda za su halarci taron daga ketare za su samu damar duba sabuwar fuskar yankin Binhai. Lallai ana jin alfahari a kansa.
Yayin da wakilinmu yake aiki a tashar jiragen ruwa ta Tianjin, ya gano cewa, tashar tana gwada kyakkyawar makoma ta birnin Tianjin mai cike da kuzari. Jami'in tashar jiragen ruwa ta Tianjin An Weibing ya furta cewa,
"Tashar jiragen ruwa ta Tianjin, tasha ce mafi girma a arewacin kasar Sin. Kuma tana kai matsayi na uku a duk fadin kasar Sin, yayin da take kai matsayi na biyar a duniya. An kasa ta zuwa kashi hudu, wato tashar Beijiang, tashar Dongjiang, tashar Nanjiang da tahsar masana'antu dake kusa kusa."
Yanzu bai fi sauran kwanaki goma ba za a kaddama da dandalin tattaunawar Davos na yanayin zafi a birnin Tianjin. An yi imani cewa za a samu babbar nasara a wannan karo. (Fatima)