in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarwarin tattalin arzikin tsakanin Sin da Japan na amfanawa kasashen biyu
2010-08-30 18:39:58 cri

A cikin wadannan shawarwari, Mr. Wang Qishan mataimakin firaministan kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin tana da babbar kasuwa, za ta ci gaba da bude kofa ga waje tare da bullo da kyakkyawan yanayin zuba jari. Wakilan kasar Japan suna ganin cewa, huldar da ke tsakanin kasashen Japan da Sin tana ta bunkasuwa, suna fatan za a sami ci gaba cikin sauri.

Game da bunkasuwar huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen biyu a nan gaba, Mr. Zhang Jifeng ya ce, akwai matsaloli guda 3 a yanzu. "Bisa cinikin da ke tsakanin kasashen biyu, yanzu yawan cinikin tsakaninsu ya yi yawa, da wuya a samu karuwa da sauri. Na biyu, yawan jarin da kasar Japan ta zuba a kasar Sin ya ragu sosai. Na uku, yawan kayayyakin da kasar Sin ke shigo daga kasar Japan ya fi wadanda kasar Japan ke shigo daga kasar Sin a dogon lokaci."

Mr. Zhang Jifeng yana ganin cewa, ra'ayi daya da kasashen biyu suka samu a shawarwari na wannan karo zai ba da taimako wajen warware wadannan matsaloli. "Da farko manyan jami'an kasashen biyu sun sami ra'ayi daya, hakan ya bullo da yanayi mai kyau wajen warware matsaloli, kuma dukkan bangarorin biyu suna son sa kaimi ga ciniki da zuba jari da ke tsakaninsu."

A ran 29 ga wata, Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya gana da wakilan kasar Japan, inda ya ce, "Kasashen Sin da Japan suna taka muhimmiyar rawa kan harkokin tattalin arzikin duniya, kuma shawarwarin da ke tsakaninsu suna da muhimmiyar ma'ana gare su har ma da kasashen duniya. Sakamakon kokarin da aka yi, bangarorin biyu sun sami kyawawan sakamako da dama, wannan zai sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakaninsu." [Musa Guo]


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China