A ran 29 ga wata da yamma, jama'a sun taru a wurin yawon shakatawa na Victoria, kuma sun yi zanga-zanga cikin lumana daga wannan wuri zuwa filin yawon shakatawa na Zheda, kuma jama'ar dake yin zanga-zanga sun yi shiru domin nuna bacin ransu.
Da karfe 3 da yamma a wannan rana, kafin fara yin zanga-zanga, 'yan majalisar dokokin yanki daga jam'iyyu daban daban sun nuna alhini har na tsawon mintoci 3 tare da masu zanga-zanga. Da karfe 3 da minti 20, jama'a suka fara yin zanga-zanga daga wurin yawon shakatawa na Victoria.(Zainab)