Mr Lavin ya bayyana wa 'yan jarida cewa, an girmama kowace kasa a bikin EXPO na Shanghai, kasa da kasa suna da dandalin nune-nune basa zaman daidai wa daida, wanda ya taimakawa masu kallo daga kasar Sin su kara fahimtar sauran kasashen duniya, kana masu kallo daga kasashen waje za su kara fahimtar kasar Sin gaba daya, wannan shi ne hanya mafi kyau ta fannin diplomasiyar dake tsakanin jama'ar kasashe.
Mr Lavin wanda ya taba zama mataimakin ministan harkokin ciniki na kasar Amurka ya furta cewa, bikin EXPO na Shanghai zai kasance wani muhimmin dandalin inganta mu'amalar al'adu dake tsakanin Sin da Amurka. An kafa rumfar kasar Amurka tare da fatan masu yawon shakatawa na kasar Sin za su gano abubuwa iri daya na kasashen biyu.(Zainab)