in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin ranar rumfar kasar Namibia a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-08-26 14:41:38 cri

A ran 26 ga wata, an yi bikin ranar rumfar kasar Namibia a farfajiyar bikin baje kolin duniya na Shanghai. Mataimakin babban wakilin gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin bikin EXPO na Shanghai Wang Yongqiu da ministan kula da ciniki da masana'antu na kasar Namibia Hage Geingob sun halarci bikin tare da yin jawabi.

Wang Yongqiu ya bayyana cewa, rumfar kasar Namibia mai taken " zaman rayuwa iri daban daban" ta bayyana hanyoyin zaman rayuwar kasar da halin da birane ke ciki da kuma aikin kiyaye muhalli da dabbobi.

Bikin EXPO na Shanghai zai sa kaimi ga kara yin mu'amala a tsakanin Sin da Namibia a fannin al'adu, da zurfafa zumunta a tsakaninsu, da kara fahimtar juna a fannin siyasa, da kuma inganta dangantakar hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi.

Mr Geingob yana fatan yin amfani da nune-nunen rumfar kasar Namibia dake shafar fannonin al'adu da tarihi da muhalli a kasar wajen kara jawo mutane zuwa kasarsa don yin yawon shakatawa da kuma zuba jari.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China