in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ranar rumfar kasar Liberia a bikin EXPO na Shanghai
2010-08-23 21:31:48 cri

A ran 23 ga wata, an yi ranar rumfar kasar Liberia a bikin EXPO na Shanghai. Mataimakin shugabar Jamhuriyar Liberia H.E.Joseph N.Boakai da mataimakin ministan al'adun kasar Sin Zhao Shaohua sun halarci bikin.

Mataimakin ministan al'adun kasar Sin Zhao Shaohua ya bayyana a gun bikin bude taro cewa, bikin EXPO na Shanghai ya samar da sabon zarafi ga kara fahimtar juna da habaka hadin gwiwa a tsakanin jama'ar kasashen Sin da Liberia.

Mataimakin shugabar Jamhuriyar Liberia H.E.Joseph N.Boakai ya nuna a cikin jawabinsa cewa, bikin EXPO na Shanghai zai zurfafa abokantakar dake tsakanin kasashen biyu, kana zai ingiza musayar ra'ayi a tsakaninsu a fannonin al'adu da wasan fasaha.

A gun bikin, kungiyar wasan fasaha ta kasar Liberia ta yi raye-raye masu ban sha'awa ga masu yawon shakatawa dake farfajiyar bikin EXPO domin nuna al'adun musamman na al'ummar kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China