A jawabin da sanata Jubril Martins-Kuye ya gabatar, ya yi bayani kan irin dimbin albarkatun kasa da Allah ya hore wa kasar Nijeriya, da kuma yadda gwamnatin kasar take kokarin bunkasa bangarori daban daban da nufin kara janyo masu zuba jari zuwa kasar. A sa'i daya kuma, sanata Kuye ya nuna yabo kan bikin EXPO na Shanghai tare da bayyana cewa, zuwansa bikin Expo zai taimakawa Nijeriya ta karu da fasahohi da yawa musamman ma ta fuskar kiyaye tsarin birane da kyautata muhalli, sa'an nan shagalin rumfar kasar da ake yi zai baiwa wasu kasashe karin damar fahimtar Nijeriya ta fannin ci gaban tattalin arziki da siyasa.
A nasa jawabin, jakada Wang Yongqiu ya bayyana kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen 2. Haka kuma ya bayyana imaninsa game da yadda kasashen 2 za su yi amfani da damar da bikin ya samar wajen habaka hadin gwiwarsu a fannoni da dama.