in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ranar rumfar Togo a bukin baje kolin duniya na Shanghai
2010-08-20 21:43:14 cri

Yau ranar 20 ga wata, an yi bikin ranar rumfar kasar Togo a taron baje kolin duniya na Shanghai. Ministan harkokin waje na Sin Yang Jiechi, da shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbe sun halarci bikin tare da yin jawabi.

Yang ya bayyana cewa, a sabon yanayi na samun bunkasuwa tare da juna da samun sauyawar tsarin duniya, a matsayin abokan arziki dake sada zumunci da hada gwiwa cikin adalci, Sin da Togo suna da babbar moriyar juna a fannin samun bunkasuwa cikin lumana. Yana fatan kasashen biyu za su karfafa dankon zumunci a tsakaninsu, da yin musayar fasahohi da samun darasi daga juna bisa bukin baje kolin duniya a wannan karo, a kokarin kara samar da kyakkyawar makoma tsakanin kasashen biyu.

Gnassingbe ya yi jawabin cewa, gwamnatin kasar Sin tana taimakawa Togo wajen raya kasa a fannoni da dama cikin dogon lokaci, tare da nuna goyon baya ga kasar wajen halartar bukin baje kolin duniya na Shanghai a fannin kudi da fasahohi da ba da hidimomi da dai sauransu. A sakamakon haka, yana godiya sosai da sosai.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China