Yang ya bayyana cewa, a sabon yanayi na samun bunkasuwa tare da juna da samun sauyawar tsarin duniya, a matsayin abokan arziki dake sada zumunci da hada gwiwa cikin adalci, Sin da Togo suna da babbar moriyar juna a fannin samun bunkasuwa cikin lumana. Yana fatan kasashen biyu za su karfafa dankon zumunci a tsakaninsu, da yin musayar fasahohi da samun darasi daga juna bisa bukin baje kolin duniya a wannan karo, a kokarin kara samar da kyakkyawar makoma tsakanin kasashen biyu.
Gnassingbe ya yi jawabin cewa, gwamnatin kasar Sin tana taimakawa Togo wajen raya kasa a fannoni da dama cikin dogon lokaci, tare da nuna goyon baya ga kasar wajen halartar bukin baje kolin duniya na Shanghai a fannin kudi da fasahohi da ba da hidimomi da dai sauransu. A sakamakon haka, yana godiya sosai da sosai.(Fatima)