in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata tura wata tawaga zuwa bikin Expo na Shanghai
2010-08-19 10:31:00 cri

Kasar Najeriya za ta tura wata tawagar data hada da kusoshin gwamnati da manyan shugabannin kamfanoni wadanda za su wakilci kasar a bikin EXPO na kasa da kasa dake gudana a birnin Shanghai a karkashin taken taron kasuwanci da zuba jarin Najeriya. Ministan kasuwanci da masana'antu, mista Jubril Martins-Kuye zai jagoranci wannan tawaga zuwa bajen kolin da aka bude 1 ga watan Mayu da za'a kuma kammala 31 ga watan Oktoba mai zuwa. "Najeriya ta shiga bikin, kuma shugaban kasarmu ya so ya samu zuwa da kansa, amma gani na zo dan in wakilce shi" inji minista gaban manema labarai a birnin Abuja.

Tawagar manyan kusoshin za ta hada sakataren dindin da kuma wasu manyan ma'aikatan da kuma daraktoci wannan ofishin. "Muna matukar murna tuni domin nuna albarkatun da kasar ke da su da kuma yadda za mu hada kai da sauran kasashe domin bunkasa kanmu ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci" ya kara da cewa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China