Bayan yakin duniya na biyu, Hepburn da mahaifiyarta suka kaura zuwa birnin London na Birtaniya. A shekarar 1951, Hepburn ta zama 'yar wasan sinima a hunkunce bisa wani fim mai suna "Laughter in Paradise". Daga bisani a kai a kai, Hepburn ta yi wasa ta shiga fina-finai da dama, kamar Roman Holiday, My Fair Lady, Breakfast at Tiffany's, War and Peace da dai sauransu. Bisa wadannan fina-finai, sunan Hepburn ya fito sosai.
Bayan da Andrey Hepburn ta tsufa, ta ci gaba da kokarin ba da gudummawa ga sha'anin jin kai. A shekarar 1988, ta zama wakiliyar asusun yara ta MDD. A matsayinta, Hepburn ta kan gudanar da bukukuwan kide-kide da ayyukan tara biliyoyin daloli, tare da jinjinawa wasu yara a yankunan dake fama da talauci. Ta taba kai ziyara a yankunan da dama dake Asiya, Afirka, Latin Amurka da dai sauransu, kamar Habasha, Sudan, Guatemala, Honduras, Venezuela, Ecuador, Bangladesh da dai makamantansu. Hepburn ta samu karbuwa daga jama'a sosai da sosai. A karshen shekarar 1992 kuma, yayin da take rashin lafiya, Hepburn ta kai ziyara a Somaliya domin jinjinawa wasu yara dake cikin tsananin rayuwa a sakamakon karancin abinci.
To, jama'a masu karanta, yanzu bayani ke nan kan tambayar malam Musa, da fatan ka duba ka gamsu da shi.
Bayan haka, a makon jiya, masu sauraronmu da yawa sun aiko mana da wasiku, kamar malama Fatima Musa Abbas a Katsina, tarayyar Nijeriya, da malam Danlawan Baba a Nijeriya, da malam Shuaibu Muhammed Rijiyar maikabi dake jihar kebbi, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda kuma ba mu samu damar karanta sakwanninsu duka ba. A sakamakon haka, muna farin ciki sosai. Da fatan masu sauraronmu za ku ci gaba da aiko mana da wasiku domin bayyana ra'ayoyinku da ba da shawarwari masu kyau. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu. (Fatima)