Wakilin NBC ya yi hira da Petraeus a wani shiri a wannan rana. Inda Petraeus ya bayyana cewa, Ben Laden ya kasance wani muhimmin mutum mai matsanancin ra'ayi, abin da ya sa kokarin cafke ko harbe shi ya zama wani muhimmin aiki ga wadanda suke aiwatar da ayyukan yaki da ta'addanci a duniya.
A sa'i daya kuma, Petraeus ya amince da cewa, yana da wuya, Ban Laden ya fito a bainar jama'a. Ya ce, Osama Ben Laden ya kan boya a tsaunuka masu nisa da iyakar dake tsakanin kasashen Afghanistan da Pakistan saboda haka ya kan shafe makonni domin watsa labarinsa.(Amina)