in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Asiya a birnin Guangzhou
2010-08-11 15:16:13 cri
Jama'a masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Kuma muna yi muku godiya sosai sabo da kokarinku na aiko da wasiku, da fatan za ku ci gaba da yin musayar ra'ayi tare da mu ta hanyoyin bugo wayar tarho, aiko da sakwanni ko E-mail da dai sauransu. Sai mun ji daga wajenku.

To, a cikin shirinmu na yau, da farko za mu karanta wasu wasikun da muka samu daga wajenku. Ga wannan sako daga malam Mohammed Idi Gargajiga a Nijeriya, inda ya rubuto mana cewa, "A madadin dukkan 'ya'yan kungiyar GOMBAWA CRI LISTENERS CLUB da ni kaina shugaban club, muna sanar da ku cewa, mun ji bakin ciki kwarai da gaske da samun mummunan labari na afkuwar bala'in ambaliyar ruwa, sakamakon zabtarewar kasa da tabo da duwatsu a yankin Gansu na kasar Sin, da ta haddasa mutuwar mutane da dama. Kuma muna mika sakon ta'aziya ga iyalai na mamatan da gwamnatin kasar Sin da sauran jama'ar kasar Sin baki daya, da fatan gwamnatin kasar ta Sin za ta kara nade kafar wando da zage damtse wajen ceton al'umma da abin ya shafa, da kara sa karfi ga aikin rigakafi ga sauran wurare da yankuna da suke bakin kura ko fuskantar bala'u daga indallahi."

Mun gode, malam Gargajiga. Yanzu muna fuskantar babbar matsalar yaki da ambaliyar ruwa a lardin Gansu. Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi rangadi a can tare da ba da umurni cewa, abin dake gaban kome shi ne ceton mutane. Mun yi imani cewa, bisa kokarin gwamnati da jama'ar kasar Sin baki daya, za mu yi nasara a karshe. Allah ya taimake mu, amin.

Sakon malam Gargajiga ke nan. Bayan haka, malam Abdou Nenne a Kirbi, jamhuriyyar Cameru ya rubuto mana cewa, "A madadin daukacin jama'ar kasar Kamaru, muna taya 'yan uwanmu na kasar Nijer murnar cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Faransa, da fatan Allah ya albarkaci kasar Niger baki daya."

To, mun gode, malam Abdou Nenne. Mu ma muna taya murnar cika shekaru 50 da samun 'yancin kan kasar Nijer daga Faransa. Da fatan kasar za ta ci gaba da samun bunkasuwa a fannin tattalin arziki, cinikayya, zamantakewar al'umma da dai sauransu. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Sakon malam Abdou Nenne ke nan. A kwanan baya, malam Issa Musa daga Bauchi, tarayyar Nijeriya ya bayyana mana cewa, "Na ji an ce za a gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Asiya a birnin Guangzhou na Sin, ko ba haka ba?"

E, haka ne, malam Musa. Za a kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Asiya a karo na 16 a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin a ran 12 ga watan Nuwamba na bana. A shekarar 2004 ne, birnin Guangzhou ya yi nasarar samun damar shirya gasar. Bisa takenta na "Maraba da zuwa gasar wasannin motsa jiki ta Asiya tare da samar da rayuwa mai kyau", yanzu ana gudanar da aikin shirya gasar yadda ya kamata. Mataimakin magajin garin birnin Guangzhou, kana mataimakin babban sakataren kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Asiya, Xu Ruisheng ya gabatar mana da cewa, yanzu an kusan kammala ayyukan shiryawa, kuma ana kokarin kammala su yadda ya kamata. Xu ya ce,

"Dukkan ma'aikatan kwamitin shirya gasar wasannin matsa jiki ta Asiya muna shirya gasar bisa iyakacin kokarinmu."

A kokarin biyan bukatun gasar a wannan karo, an kara kafa dakunan matsa jiki 12 a birnin Guangzhou, inda ake da dakunan motsa jiki 60 a da. Kuma ana kokarin haye wahalhalu da dama na karancin lokaci da gamuwa da matsaloli da yawa da dai sauransu. A yayin kafa wadannan dakuna, an fi gamuwa da matsaloli a dakin Yayun, babban dakin motsa jiki a birnin Guangzhou, wanda ya hada da dakunan musamman da dama a ciki. Shugaban hukumar fasali ta ofishin kula da manyan ayyukan birnin Guangzhou Deng Xinyong ya bayyana cewa,

"Mun fara gina wannan dakin a watan Nuwamba na shekarar 2008 a hukunce. Kuma mun kiyasta cewa, za a kammala a karshen watan Agusta na bana. Wannan ne dakin motsa jiki mafi girma a birnin Guangzhou."

An yi kiyasin cewa, za a kammala ginadukkan dakunan cikin lokaci. Bayan haka, a yayin kafawa, kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Asiya ya yi la'akari da cewa, kamata ya yi mazaunan wurin su ci gajiyar sakamakon gasar. Xu Ruisheng ya bayyana cewa, gasar a wannan karo za ta samarwa birnin Guangzhou al'adun gasar wasannin motsa jiki ta Asiya da za a gada masu daraja sosai. Ya furta cewa,

"Yayin da muke gina wadannan dakunan motsa jiki, mun yi la'akari da cewa, kamata ya yi jama'a su ci gajiyarsu. Yayin da muke yin fasali da kuma zaben wurare, mun dora muhimmanci cewa, dukkansu za su dace da bunkasuwar birnin da biyan bukatar mazauna ta fannin motsa jiki. Mun karfafa amfaninsu a fannoni da dama, da kyautata manyan ayyuka dake kewayensu."

A cikin kowace gagarumar gasar wasannin motsa jiki, ba za a rasa goyon baya daga masu aikin sa kai ba. Bisa wani labarin da aka bayar, an ce, kawo yanzu dai, mutane sama da dubu 900 sun yi rajistar zama masu aikin sa kai na gasar wasannin motsa jiki ta Asiya da ta nakasassu. Ma Lanzi, daliba ce ta jami'ar Zhongshan ta gaya mana cewa, Ko da yake masu aikin sa kai suna gajiya sosai, amma a sa'i daya suna jin dadi kwarai. Ma ta furta cewa,

"A yayin babban taro tsakanin shugabannin tawagar kasa da kasa ta gasar wasannin motsa jiki ta Asiya, mun gudanar da ayyukan hidima a jere har na tsawon kwanaki hudu. A kowace rana, mu kan huta na tsawon awoyi 5 zuwa 6 kawai. Dalibai hurhudu daga birnin Zhuhai su kan zauna a daki daya, akwai wahala sosai. Duk da haka, yayin da muka ji babban yabon da majalisar kula da gasar wasannin motsa jiki ta Asiya da jami'an kwamitin kula da gasar na kasa da kasa suka yi mana, dukkanmu mun yi farin ciki kwarai da gaske. A ganinmu, wannan ya dace da gajiyarmu."(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China