in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wake-wake da raye-raye ta jamhuriyar Niger ta yi al'ajabi da bikin baje-koli na Shanghai
2010-08-04 17:11:46 cri

Yayin da shugaban tawagar wake-wake da raye-raye ta jamhuriyar Niger Tijani Ali ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, "na yi al'ajabin ganin, akwai kasashe da dama da suka shiga cikin bikin baje-koli na Shanghai kuma an samu masu yawon shakatawa da yawa.

An kafa tawagar wake-wake da raye-raye ta jamhuriyar Niger a shekarar 1974, kuma tawagar wake-wake da raye-raye ta jamhuriyar Niger, wata shahararriyar tawagar masu wasan fasahohi ce ta birnin Niyame hedkwatar kasar Niger.

Tijani ya ce, ina yin al'ajabi da bikin baje-koli na Shanghai, sabo da an hada al'adu na kasashe da dama a gun bikin, kuma an nuna halaye na musamman na kasashen duniya, wanda ya jawo hankalin jama'a sosai. Tawagar wake-wake da raye-raye ita ma za ta yi iyakacin kokarinsu domin nuna jamhuriyar Niger ga duk duniya. A sa'i daya kuma ya bayyana cewa, yana fatan ziyararsa a kasar Sin za ta kawo sakamako mai kyau, inda na farko za a kara kokarin fahimtar da jama'ar Sin game da tarihi da al'adun Niger, domin sa kaimi ga dankon zumunci na kasashen biyu, sai kuma a inganta mu'amala da tuntubar masu wasan fasahohi na kasar Sin, domin koyon fasahohi wajen nuna wasanni a tsakaninsu, a karshe, ya kamata a yi kokari domin gina wani tsari, don samun damar nuna wasanni a kasar Sin.

A ranar 3 ga wata, an yi bikin murnar ranar rumfar jamhuriyar Niger a gun bikin Expo na Shanghai, kuma tawagar wake-wake da raye-raye ta jamhuriyar Niger ta gabatarwa baki na kasashen Sin da Niger da raye-raye na gargajiya na kananan kabilu 2 na jamhuriyar Niger, kuma 'yan kallo sun yi al''ajabi game da al'adu na kasashen Afrika, a cikin makwanni 2 masu zuwa, tawagar wake-wake da raye-raye za ta ci gaba da nuna wasanni masu kayatarwa ga masu yawon shakatawa a rumfar hadin gwiwa ta kasashen Afrika, kuma tabbas ne wasanninsu za su burge 'yan kallo na kasar Sin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China