Sanusi: A kwanan baya, wakilinmu ya ziyarci Dr. Dong Ke, wani injiniya da ke aiki a hukumar tsara shirin raya biranen kasar Sin domin neman dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta dauki wannan mataki na daidaita wasu kananan hukumomi a wasu manyan birane. Dr. Dong Ke ya bayyana cewa, "Lokacin da ake tsara shirin raya wani birni, a kan jaddada samun daidaito a tsakanin kokarin samar da yankunan dake neman ci gaba da nauyin da ya rataya a wuyan kananan hukumomi. Amma yanzu, lokacin da ake neman ci gaba a wani birni, a kan gano cewa, ba a iya samun irin wannan daidaito ba. Alal misali, a kan kafa kananan hukumomi guda biyu a wani karamin yanki. Sabo da haka, a kan samu matsaloli a tsakaninsu."
Ibrahim: Dr. Dong Ke ya ce, dalilan da suka sanya daidaita kananan hukumomi a biranen Beijing da Tianjin da Xiamen da Shanghai shi ne "Wani dalili shi ne, kamar a nan birnin Beijing, an daidaita kananan hukumomi a cikin gari domin kokarin raya yankunan cikin gari. Yanzu ba a bukatar samar da karin ayyuka a cikin garin Beijing, sabo da haka, an samu damar hada su da wasu kananan hukumomi. Sannan kamar a birnin Shenzhen da na Tianjin, an aiwatar da manufofi daban daban a cikin garin da karkararsu a da. Bayan an daidaita kananan hukumominsu, yanzu za a iya aiwatar da manufofi iri daya a dukkan yankunansu. Sannan a biranen Shanghai da Chongqing, dalilin da ya sa aka kafa sabbin kananan hukumomi shi ne gwamnatin kasar Sin tana son aiwatar da sabbin manufofin neman ci gaba a wadannan birane biyu."
Sanusi: Ko da yake akwai dalilai daban daban da suke kasancewa a lokacin da ake daidaita kananan hukumomi, amma a ganin shehun malami Jiao Hongchang, wanda yake aiki a jami'ar koyon ilmin dokoki na kasar Sin, bayan da aka daidaita kananan hukumomi a manyan birane, za a iya samun damar kara saurin raya tattalin arziki da kuma yin tsimin kudin da ake kashewa a hukumomin gwamnati. Mr. Jiao Hongchang ya ce, "Wani muhimmin dalilin da ya sa aka daidaita kananan hukumomi shi ne kokarin raya tattalin arziki. Bayan da aka samu bunkasuwar tattalin arziki, a kan gamu da cikas kan huldar da ke kasancewa a tsakanin kananan hukumomi da shirin raya tattalin arziki. Alal misali, a cikin garin wani birni, kananan hukumomi biyu su kan yi kokarin neman samun ayyuka daya, har ma dukkan kananan hukumomin wani birni suna son samun irin wannan ayyuka a lokaci guda. Sannan za a iya yin tsimin kudin da ake kashewa a kananan hukumomin gwamnati da kuma kammala aikin cikin hanzari."
Ibrahim: Haka kuma shehun malami Jiao Hongchang ya nuna cewa, ba ma kawai aikin daidaita kananan hukumomin manyan birane zai iya samar da wata sabuwar dama ta raya tattalin arziki ba, har ma zai iya kawo moriya ga zaman al'umma. Mr. Jiao ya kara da cewa, "Ba ma kawai tsarin yana kawo moriya ga tattalin arziki ba, har ma zai kawo moriya ga zaman al'umma. Alal misali, yankunan arewacin birnin Beijing su kan samu ci gaba cikin sauri, amma yankunan kudancinsa su kan samu ci gaba sannu a hankali. Bayan da aka hada yankunan arewa da na kudancin birnin, za a iya kara samun damar raya yankunan kudancin birnin a fannoni daban daban."
Sanusi: Bayan da aka yi kwaskwarima kan kananan hukumomin da ke cikin wani babban birni, ko hakan zai yi tasiri ga shirin raya wannan birni? A watan Janairu, an kafa wata sabuwar karamar hukuma a birnin Tianjin wadda ke kunshe da tsoffin kananan hukumomi uku. Mr. Yin Hailin, direktan hukumar tsara shirin raya birnin Tianjin ya bayyana cewa, "Bayan da aka hada wadannan kananan hukumomi uku suka zama karamar hukuma guda, yanzu babu wasu sauye-sauye sosai a unguwannin mazauna, amma sauyin da ya fi muhimmanci shi ne za mu iya daidaita ayyukan yau da kullum da za a samar a yankunan da ke karkashin mulkin wannan sabuwar karamar hukuma. Ba mu bukatar samar da ayyukan yau da kullum iri daya a kananan hukumomi daban daban da suke dab da juna."
Ibrahim: Hakika, ba ma kawai matakin daidaita kananan hukumomi a wani babban birnin zai iya samar da damar bunkasa tatttalin arziki da zaman al'umma a wannan birni ba, har ma zai iya kawo moriya ga kokarin kyautata aikin samar da ayyukan yau da kullum. Amma ko shakka babu dole ne a kara mai da hankali kan wasu matsalolin da za su iya kunno kai sakamakon daidaita irin wadannan kananan hukumomi. (Sanusi Chen)