in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Yantan na kokarin raya masana'antu marasa gurbata muhalli
2010-07-29 19:29:26 cri
Ibrahim: Birnin Yantan birni ne mai arzikin albarkatun halittu kuma mai saukin zirga-zirga da ke bakin teku a lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin. Kuma yana daya daga cikin muhimman sansanonin masana'antun lardin Shandong. Tun daga shekara ta 2008, birnin Yantan ya fara kokarin yin kwaskwarima ga tsarin masana'antun dake yankin, kuma yana sa kaimi kan masana'antu da su yi kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani domin raya masana'antu marasa gurbata muhalli wadanda suke tsimin makamashi. A cikin shirinmu na yau, za mu karanta muku wani bayani kan yadda birnin Yantan yake raya tattalin arzikin da ba sinadarin Carbon sosai.

Sanusi: Jama'a masu sauraro, wannan wata murya ce da aka dauka a yayin kaddamar da bikin EXPO na Shanghai yau kusan watanni 3 da suka gabata. A birnin Yantan mai nisan kilomita dubu 1 da birnin Shanghai, Mr. Yu Zhenhua, shugaban kamfanin samar da kayayyakin lantarki mai suna Gabas ya kalli wannan biki ta talibijin. Ba ma kawai yana farin ciki ba, bikin EXPO na Shanghai yana da muhimmiyar ma'ana ta daban, wato kamfaninsa ya samar da na'urorin samar da wutar lantarki na ko ta kwana ga farfajiyar bikin EXPO na Shanghai. Irin wadannan na'urorin samar da wutar lantarki suna tsimin makamashi, kuma ba su fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Mr. Ding Zhenhua ya ce, "Manufofin yin tsimin makamashi da kuma rage fitar da abubuwan gurbata muhalli da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ke aiwatarwa sun zama wani muhimmin nauyin da ke bisa wuyan gwamnatocin dake matakai daban daban na kasar. Musamman bayan abkuwar rikicin hada-hadar kudi a duniya, kamfanoni wadanda suke amfani da makamashi da yawa sun fi son yin amfani da na'urorin tsimin makamashi. Yanzu su da kansu ne suke zuwa kamfaninmu a kullum."

Ibrahim: A hakika dai, tun daga watanni 6 na karshen shekarar 2008, kamfanonin da suke samar da injuna da na'urorin tsimin makamashi kamar kamfanin Gabas na kasar Sin sun fara kokarin neman ci gaba sakamakon aiwatar da manufofin raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Mr. Sun Yongchun, sakataren kwamitin birnin Yantan na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin yana ganin cewa, yanzu an riga an canja ka'idojin raya tattalin arziki, inda Mr. Sun ya ce, "A da, ana kokarin ci gaba ne bisa albarkatun halittu da kuma yin amfani da su sosai. Sakamakon haka, idan ka samu ci gaba cikin sauri sosai, tabbas ne a yi hasara sosai a fannoni daban daban. Da zaran an kara saurin yin watsi da injuna da na'urorin da suke da koma baya, kuma aka kara saurin raya tattalin arzikin da babu sinadarin Carbon a cikinsa, hakika za a iya daidaita duk wani sabani da sauran batutuwa iri iri da suke kasancewa a gabanmu."

Sanusi: Ya zuwa yanzu, yawan masana'antun da suke amfani da sabon makamashi ya kai fiye da 50, kuma yawan darajar kayayyakin da suke samarwa ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 1.5 a kowace shekara. An yi hasashen cewa, jimillar GDP da masana'antun birnin Yantan za su samu zai kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 420 sakamakon samar da kayayyaki masu kunshe da fasahohin zamani, wato zai karu da kashi 11 cikin dari.

Ibrahim: Bugu da kari, birnin Yantan yana kokarin rage fitar da abubuwa masu gurbata yanayin duniyarmu. Mr. Jiang Ming, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da sadarwa na birnin Yantan ya bayyana cewa, dole ne a dauki kwararan matakan rufe masana'antu wadanda suke fitar da abubuwa masu gurbata yanayin duniyarmu. Mr. Jiang ya ce, "Idan mun dauki matakan rufe kananan kamfanonin samar da wutar lantarki masu aiki da kwal, kuma idan aka gina wani babban kamfanin samar da wutar lantarki mai aiki da kwal kawai, lallai ba za mu iya rage jimillar abubuwa masu gurbata yanayin duniyarmu ba. Sabo da haka, dole ne mu kyautata da kuma daidaita tsarin sana'o'i domin cimma burin rage yawan abubuwa masu gurbata yanayin duniyarmu."

Sanusi: Sabo da birnin Yantan yana bakin tekun Pacific, a cikin shekarun da suka shude, ana kokarin raya tattalin arzikin da ke shafar teku. Mr. Sun Yongchun, sakataren kwamitin birnin Yantan na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Lokacin da ake tattaunawa kan aikin daidaita tsarin masana'antu da canja hanyar neman ci gaba, mun gane cewa, dole ne a dogara da sabbin fasahohin zamani da aka kirkiro domin neman hanyar raya sabbin sana'o'i." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China